Tauhidi ginshikin Musulunci (2)
Babi na Uku Wanda ya tabbatar da Tauhidi zai shiga Aljanna ba tare da bincike ba Allah Yana fadi a cikin Alkur’ani Mai girma: “Hakika Annabi Ibrahim ya kasance al’umma ce saboda kaskantar da kansa ga Allah da sallama al’amarinsa baki daya ya bar duk wata hanya ta shirki da Allah, kuma bai kasance cikin […]
Babi na Uku Wanda ya tabbatar da Tauhidi zai shiga Aljanna ba tare da bincike ba Allah Yana fadi a cikin Alkur’ani Mai girma: “Hakika Annabi Ibrahim ya kasance al’umma ce saboda kaskantar da kansa ga Allah da sallama al’amarinsa baki daya ya bar duk wata hanya ta shirki da Allah, kuma bai kasance cikin mushrikai ba.” (Nahli, 120). Mai girma da daukaka kuma Ya ce dangane da wadanda za su shiga Aljanna: “Su ne wadanda ba su yi shirki da Ubangijinsu da komai ba.” (Al-Muninun, 59).
An ruwaito wani Hadisi daga Husaini dan Abdurrahman ya ce: “Wata rana ina zaune wajen Sa’idu dan Jubairu sai ya ce min: “Wane ne ya ga tauraruwar da ta fadi jiya? Sai na ce: “Na gan ta, amma ba Sallah nake yi ba lokacin da na ganta sai dai abin da ya sa ban yi barci ba kunama ce ta harbe ni. Sai ya ce, to me ka yi lokacin da kunamar ta harbe ka? Sai na ce: Tofi na yi,” Sai ya ce me ya sa ka yi tofi? Sai na ce abin da ya sa na yi tofi saboda labarin da Sha’abiyyu ne ya ba ni. Sai ya ce ‘to da kai da Sha’abiyyun din wane ne ya fada muku ya hallata a yi tofi? Sai na ce masa Buraida dan Husaib ya ba mu labari ya hallata a yi tofi a waje biyu kawai. Wuraren su ne don kambun baka da kuma dafi. Sai ya ce “Lallai wannan labari naka haka yake sai dai ni abin da na ji daga Ibn Abbas (RA) shi kuma daga Annabi (SAW) ya ce, an nuno min wadansu jama’a da Annabi a cikinsu sai aka kara nuno min wadansu mutum uku da Annabi a cikinsu, sai kuma aka nuno min wani Annabi shi kadai ba kowa tare da shi. Sai na sake ganin wadansu jama’a masu yawa, sai na tambaya, wadannan al’ummata ce ko? Sai aka ce min Annabi Musa ne da jama’arsa. Sai na kara dubawa sai ga kuma wadansu jama’a masu yawa. Aka ce min wadannan ne al’ummarka. Sai aka ce min bayan su akwai wadansu dubu saba’in daga al’ummata za su shiga Aljanna ba tare da bincike ba ko azaba.” Sai Annabi (SAW) ya tashi ya shiga gida. Sai sahabbai suka yi hira a tsakaninsu a kan su wane ne wadannan dubu saba’in din? Wadansu suka ce kila sahabban Annabi (SAW) ne, wadansu kuma suka ce kila wadanda aka haifa ne cikin Musulunci ba su taba shirki ga Allah da kowa ba. Sai suka yi ta muhawara a tsakaninsu kan su wane ne dubu saba’in din nan. Suna cikin haka sai Annabi (SAW) ya fito, suka ba shi labarin muhawarar da suka yi. Sai Annabi (SAW) ya ce “Su ne wadanda ba su yi tofi a cikin rayuwarsu ba, kuma ba su yi lalas ba, kuma ba su yi camfi ba, su ga Allah kawai suka dogara. Nan take sai wani sahabi mai suna Ukasha Ibn Muhsin ya ce, “Annabi a roka min Allah Ya sanya ni cikin dubu saba’in din nan.” Sa Annabi (SAW) ya ce, “kana ciki.” Sai wani sahabi ma ya ce “Ni ma Annabi ka roka min in zama cikin wadannan dubu saba’in din.” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ai Ukasah ya riga ka.” 3
Babi na Hudu
TSORATARWA AKAN SHIRKA
Allah Yace acikin Al-Kur’ani mai girma, “Hakika Allah baya gafartawa idan akayi shirka dashi aka mutu akan haka , amma ya kan gafarta laifi wanda ba shirka ba ga wanda Yaso.” (Nisa’i, 48). A wata ayar kuma Annabi Ibrahim da kansa yana neman tsari da shirka inda yake cewa, “Ubangiji Ka nisantar da ni da ‘ya’ya na kar mu bautawa gumaka.” (Ibrahim, 35).
A wani Hadisi Annabi yana cewa, “Abin da nafi tsoro ga al’ummata, karamar shirka”. Sai aka tambayi Annabi, a shirka ma akwai karama? Sai Annabi yace, “Akwai ita ce riya (watau yin abu ba don Allah ba)”. Shi kuma Ibn Mas’ud (R.A) yace, Annabi yace, ‘Wanda ya mutu yana hada Allah da wani to dan wuta ne”. (Bukhari ya ruwaito). Amma ruwayar Muslim yace, daga Jabir (R.A) cewa, Annabi (S.A.W) yace, “Wanda ya sadu da Allah bai yi tarayya da Shi da kowa ba zai shiga aljannah, alhali kuma wanda ya sadu da Shi yana mai shirka da Shi, to dan wuta ne”.
Babi na Biyar
KIRAN MUTANE ZUWA GA KALMAR ‘LA’ILAHA ILLAL-LAHU’
Allah (S.W.T) Yana cewa a cikin Al-Kur’ani: “Ka fada (ya Muhammad (S.A.W) wannan itace hanyar ka ta kira zuwa ga Allah bisa fahimta da basira kai da wanda ya bika kuma kai baka cikin masu tarayya da Allah.” (Yusuf, 108).
An samu Hadisi daga Ibn Abbas (R.A) cewa Annabi ya aiki Mu’azu zuwa Yemen, sai yace masa, “Zaka je wajen mutanen da aka basu littafi. To farkon abin da zaka kirasu suyi imani da shi shine cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.” A wata ruwaya kuma an ce masa, “Farkon abinda zaka fara kira a kai su kadaita Allah da bauta. Idan suka yarda, ka fada musu Allah Ya wajabta sallah biyar akansu dare da rana. Idan sun yarda, ka kuma kara sanar dasu Allah Ya wajabta musu zakka wanda mawadaci zai fitar ya baiwa matalauci. Idan suka yarda suka bika akan haka, to kar ka karbi manya – manyan dukiyoyin su ba tare da wani dalili ba. Idan kayi haka kayi zalunci idan ko kayi zalunci ka ji tsoron addu’ar wanda aka zalunta don babu shamaki tsakaninta da Allah.” (Bukhari da Muslim suka ruwaito).
Wani Hadisi kuma daga Sahlu dan Sa’adi (R.A) yace, Manzon Allah (S.A.W) yace, a ranar da za’a tafi yakin Khaibara, “Gobe zamu bada tuta ga mutumin da yake son Allah da Manzonsa kuma Allah da Manzonsa suna son sa, kuma Allah zai bada nasara ta hannunsa”. Sai mutane suka kwana suna ta muhawara, wai wa za’a ba wannan tutar ne? Gari na wayewa, sai suka yi asubanci zuwa ga Annabi (S.A.W) kowanne daga cikin sahabbai yana burin da shi aka baiwa tutar. Sai Annabi yace, “Ina Aliyu dan Abi Talib?” Sai aka ce idonsa yana ciwo. Sai Annabi yace aje azo dashi. Sai aka zo da shi.Sai Annabi Yayi masa addu’a a idanunsa sai ya warke kamar bai taba rashin lafiya ba. Sai Annabi ya bashi tuta yace, ‘ka tafi a hankali har ka sauka a filin abokan gaba sannan ka kira su zuwa ga Musulunci. Ka basu labari da abinda Allah ya wajabta a kansu na hakkin Allah. Wallahi! Allah Ya shiryar da mutum daya ta hannunka shi yafi maka alheri da jajayen rakuma.”
Babi na Shida
TAFSIRIN TAUHIDI DA KUMA KALMAR ‘LA’ILAHA ILLALLAHU
Allah yace, “Wadanda kuke kira suna neman saduwa da Ubangiji ne ta kyakkyawar hanya. To, wanene suka fi shiriya kuma suka fi kusanci ga Allah? Domin su suna kaunar rahamar Ubangiji kuma suna tsoron azabar Sa. Lallai azabar Ubangiji abar tsoro ce.” (Isra’i, 57). 4 A wata ayar kuma Allah Yana cewa, akan labarin Ibrahimu (A.S). “Ka ambatawa al’ummarka (ya Muhammad) labarin Annabi Ibrahim lokacin da ya cewa mahaifinsa da jama’arsa ‘Ni baruwana da ku da duk abinda kuke bautawa sai dai wanda Ya hallicce ni. Shi kuma a sannu zai shiryar da ni kuma Ya sanya wannan kalmar tabbatacciya ga ‘ya’yansa. Yayi haka ne ko mutanensa zasu dawo su shiriya.” (Zukhruf, 26). Allah ya kara cewa, “Akwai wadansu mutane (Yahudawa da Nasara) sun bar Allah sai suka riki malamansu da fada-fadansu abokanan tarayya ga Allah.’’ (Tauba, 31). Allah kuma Yana cewa, “Akwai daga cikin mutane masu rike wadansu ba Allah ba suna sonsu kamar yadda suke son Allah. Amma wadanda suka yi imani su ba haka suke ba domin suna nuna tsananin soyayya ne ga Allah shi kadai.” (Bakara, 165).
An samu Hadisi daga Annabi (S.A.W.) ya ce: “Duk wanda yace ‘La’ilaha illal-Lahu ya kafircewa duk wani abin bauta ba Allah ba, to haram ne a ci dukiyarsa kuma haram ne a zubarda jininsa. Sakamakon sa yana ga Allah Mai Girma da Buwaya.”