Tauhidi ginshikin Musulunci (5)

Ba zan iya amfana muku komai a wajen Allah ba”. Sai ya kira Abbas (xan baffansa) ya ce, “Ba zan iya amfana maka komai a wajen Allah ba”. Sai ya kira Safiyya (‘yar uwar mahaifiyarsa) ya ce, “Ba zan iya amfanar maki komai wajen Allah ba”. karshe kuma sai ya kira ’yarsa ya ce, “Ya […]

Tauhidi ginshikin Musulunci (5)

Ba zan iya amfana muku komai a wajen Allah ba”. Sai ya kira Abbas (xan baffansa) ya ce, “Ba zan iya amfana maka komai a wajen Allah ba”. Sai ya kira Safiyya (‘yar uwar mahaifiyarsa) ya ce, “Ba zan iya amfanar maki komai wajen Allah ba”. karshe kuma sai ya kira ’yarsa ya ce, “Ya Fatima, idan kina da bukata ta dukiya, ki tambaye ni abin da kike so. Idan ina da shi zan ba ki, amma ba zan iya amfana miki komai wajen Allah ba.”

BABI NA GOMA SHA SHIDA

 Abin da ke faruwa ga Mala’iku Idan Allah ya yi  magana  Idan Allah (S.W.T) Ya yi magana Mala’iku sukan tsorata har ma su suma. Domin haka ne Allah Ya ba da labari a cikin Suratul-Saba, “Idan aka zare wannan tsoron daga zukatansu (Mala’iku) sai su ce wa Jibrilu, ‘me Ubangji Ya faxa?” Sai Jibrilu ya ce ‘Allah Ya faxi gaskiya, domin Shi Maxaukaki ne, Mai Girma”. 

An samu Hadisi daga Abu Huraira, Annabi (S.A.W) ya ce, “Idan Allah Ya hukunta wani al’amari a sama, Mala’iku sai su faxi da fukafukansu don kaskantar da kai ga zancen Allah domin suna jin maganar kamar wata sarka ce aka ja a kan falalen dutse. Wannan karar tana sanya su suma har idan suka farka daga wannan sumar sai su ce ‘me ubangijinmu Ya faxa?” Sai Jibrilu ya ce, ‘Allah Ya faxi gaskiya domin Shi ne Maxaukaki, Mai Girma’. To a wannan lokaci ne aljannu masu satar ji suke satar ji, kuma su faxa wa na kusa da su. Har ma lokacin da Sufwan yake siffantawa sai ya buxe tsakanin yatsunsa, wani a kan wani ya ce haka suke yi. Watau na sama ya faxawa na kasa da shi har su faxa wa boka ko xan duba. Shi kuma idan ya tashi zai faxa sai ya kara karya xari. 

To amma, wasu aljannun kafin su kai labari, taurari suna kona su. Waxansu kuma suna isar da labarin har zuwa ga boka. Domin haka sai ya haxa da wannan gaskiyar guda xaya da karya xari. Idan idan ya faxa musu (mutane) wannan gaskiya suka ga abin ya faru, to duk abin da ya faxa musu sai su gaskata shi. Ko da wani zai karyata a cikinsu, sai waxansu su ce masa ‘ba ya faxa mu na kaza ba kuma abin ya faru? Domin haka duk abin da ya faxa gaskiya ne. Da haka suke gaskata bokaye. Amma ruwayar Nawwas xan Sam’ana (R.A.) ya ce, Annabi (S.A.W) ya ce, “Idan Allah Yana so Ya aiko da wani umarni, to sai Ya yi magana ta hanyar wahayi. Lokacin da Ya yi wannan maganar sai sama ta yi motsi mai tsanani don tsoron Ubangiji Mai Girma da xaukaka. To, idan Mala’iku suka ji wannan magana ta Ubangiji sai su ma su faxi suna masu sujjada ga Allah. Farkon wanda zai daga kansa shi ne Jibrilu, sai Allah Ya faxa masa sakon da Yake so Ya aike shi da shi da abin da Allah Yake so. Sai Jibrilu ya zo ya wuce Mala’ikun domin kai wannan sakon. Ko wacce sama ya zo zai wuce sai Mala’ikun saman su tambaye shi, ‘me Ubangijin mu ya faxa ya Jibrilu?” Sai Jibrilu ya ce musu ‘Allah Ya faxi gaskiya domin Shi ne Maxaukaki Mai Girma’. Sai Mala’iku baki xayansu su ce, “Allah Ya faxi gaskiya. Shi Mai Girma ne, Maxaukaki’, har dai Jibrilu ya isar da wahayi ga wanda aka umurce shi da ya kai wa. 

BABI NA GOMA SHA BAKWAI

CETO:

Allah Ya ce, “ka yi gargaxi da shi (Alkura’ni) ga waxanda suke tsoron a tada su gaban Ubangijinsu ba su da wani waliyyi koma bayan Allah, balle wani mai ceto, ko kwa ji tsoron Allah.” (An’am, 51). Amma a Suratul Zumar, Allah Ya ce, “Ceto baki xaya naSa ne”. (Zumar, 44). A wata ayar kuma Allah Yana cewa, “Babu wani mai yin ceto a wajenSa sai da izininSa.” (Bakara, 255). A wata ayar Allah Yana cewa, “Da yawa mala’iku a cikin sama da kasa ba su da ikon ceton kowa sai bayan Allah Ya yi izini ga wanda Yake so, Ya kuma yarda da Shi.” (An-Najmi, 26). Allah Ya ce a wata ayar, “ku kira waxanda kuke kira koma bayan Allah waxanda ba su mallaki ko kwayar zarra ba a sama da kasa, kuma ba su da wani tarayya da Allah a sama da kasa, kuma ba su da wani mai taimako, kuma fa ceto ba zai yi amfani ba sai ga wanda Allah Ya yi wa izini”. (Saba, 22). (Waxannan ayoyi sun tabbata mana akwai ceto kenan bayan Allah Ya yi izini). Kamar yadda Abul Abbas Ibn Taimiyya ya fassara wannan ayar da ke cikin Suratul Saba ya ce: “Allah Ya kore duk wani abin da mushirikai suke haxawa da Shi. Na farko Allah Ya kore mulki ga waninSa, Ya kore rabo ga waninSa ko mai taimako gareshi. Allah Ya kore duk waxannan abubuwa guda uku sai Ya tabbatar da na huxu, shi ne ceto. Ya ce akwai amma ba zai yi amfani ba sai wanda Allah ya yi masa izini-kamar yadda ya zo a Suratul Ambiya’. “Ba za su yi ceto ba sai wanda Allah Ya yi masa izini”. (Ambiya, 28). 

To shi wannan ceto wanda masu tarayya da Allah suke cewa akwai shi korrare ne kamar yadda Alkur’ani ya bada labari. An ruwaito Hadisi daga Annabi (S.A.W) da cewa zai zo idan aka yi kiyama ya yi sujjada ya kuma gode wa Ubangiji. Shi ma Annabi da zai yi ceto ba da ceton yake farawa ba tukunna sai ya yi sujjada ga Allah sannan Allah Ya ce, “Xaga kanka ka faxi damuwarka, ana ji kuma ka roki abin da kake so an ba ka ka yi ceto ga wanda kake so ka ceta, an ba ka”. Domin tabbatar da wanda zai samu ceton Annabi sai Abu Huraira ya ce, “Wane ne zai samu cetonka ya Manzon Allah? Sai Annabi ya ce, “Wanda ya ce ‘La’ilaha illallahu’ kuma bai yi shirka ba”. To da wannan za mu gane cewa ceton Annabi yana nan, amma fa ga waxanda suka tsarkake aikinsu domin Allah Shi kaxai, kuma sai da yardar Allah. Sannan wannan ceton ba ya kasancewa ga wanda ya yi tarayya ga Allah.

Hakikanin ceto, Allah ne Ya fifita waxansu bayinSa da shi waxanda suka yi sabo amma bai kai shirka ba, sai Allah Ya gafarta musu saboda addu’ar wanda aka yi wa izini domin Allah Ya girmama shi, Ya kuma samu matsayi abin yabo.

Ceton da Alkur’ani ya bayyana babu shirka a ciki. Domin haka ne ma ya tabbatar da ceton da izinin Allah za a yi a wurare da yawa. Kuma Annabi (S.A.W) ya bayyana cewa ceton ya takaitu ne ga masu tauhidi, waxanda suka tsarkake Allah da bauta.