Tauhidi ginshiqin Musulunci (12)
DSP Imam Ahmad Adam Kutubi Babi na Arba’in da Uku: Duk wanda aka hada shi da Allah to ya yarda: Sayyidina Umar bin Khattab (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Kada ku rantse da iyayenku. Wanda kuma aka ba shi labari kuma aka rantse masa da Allah, to ya yarda da wannan rantsuwar. Wanda […]
DSP Imam Ahmad Adam Kutubi
Babi na Arba’in da Uku: Duk wanda aka hada shi da Allah to ya yarda: Sayyidina Umar bin Khattab (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Kada ku rantse da iyayenku. Wanda kuma aka ba shi labari kuma aka rantse masa da Allah, to ya yarda da wannan rantsuwar. Wanda aka rantse masa da Allah ya ki yarda, to, Allah ba ruwanSa da shi.” (Ibn Majab ya ruwaito da isnadi mai kyau).
Babi na Arba’in da Hudu:
Hani kan cewa “saboda Allah da wane ne bukatata ta biya: An samu Hadisi daga Kutailata (RA) cewa wani Bayahude ya zo wajen Annabi (SAW) ya ce, “Ai kuma ya Rasulallahi kuna shirka domin kuna cewa Allah da Muhammadu (SAW) suka tabbatar da kaza, kuma idan rantsuwa ta kama kuna rantsewa da Ka’aba.” Sai Annabi (SAW) ya fada wa sahabbai, “Idan za ku yi rantsuwa kada ku ce, ‘Na rantse da Ka’aba amma kuna iya cewa ‘na rantse da Ubangijin Ka’aba kuma kuna iya cewa ‘Allah ne Ya tabbatar min da kaza sannan kuma kai ne dalili.” (Nisa’i ya ruwaito).
An samu wani Hadisin daga Kutailata (RA) har yanzu ya ce, daga Ibn Abbas (RA) ya ce, wani mutum ya ce wa Annabi (SAW), “Allah Ya so kuma ka so.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Ai ka sanya ni abokin tarayya ga Allah ke nan. Ka ce “Allah Ya so kawai Shi kadai.”
An samu Hadisi daga dufail (RA), shi kuma dan uwan Aisha (RA) ne ta wajen mahaifiya, ya ce, “Na yi mafarkin na je wajen wadansu Yahudawa sai na ce ai ku mutane ne nagari, sai dai laifinku shi ne kuna cewa Uzairu dan Allah ne.” Sai Yahudawan suka ce kuma mutanen kirki ne sai dai laifinku shi ne kuna cewa “Allah da Muhammadu sun tabbatar da kaza.” Sai na tafi wajen Nasara kuma na ce musu: “Ku mutanen kirki ne sai dai laifinku shi ne kuna cewa Isah (AS) dan Allah ne.” Sai Nasaran suka ce min ai kuma mutanen kirki ne, sai dai laifinku shi ne kuna cewa, “Allah da Muhammadu ne suka tabbatar da kaza.” To da gari ya waye sai na tafi na fada wa Annabi (SAW) wannan mafarki nawa. Sai Annabi (SAW) ya tambaye ni, “Ka fada wa wani wannan labarin kuwa? Sai na ce “eh,” na fada ya Rasulallah (SAW). Sai Annabi (SAW) ya tsaya ya gode wa Allah ya kuma yabe shi. Sai ya ce bayan haka, “Ya ku bayin Allah! Hakika dufailu ya yi mafarki wanda har ya ba wadansu daga cikinku labari. Kuna fadar kalmarda na hana ku fada. Shi ne kuna cewa “Allah da Annabi ne suka tabbatar da kaza (wato ni da Allah ke nan muka yi abin. (To yin haka kuskure ne). Sai dai kuna iya cewa “Allah Shi kadai Ya tabbatar da abin.”
Babi na Arba’in da Biyar:
Wanda ya zagi zamani ya zagi Allah:
Allah (SWT) Ya ba da labari dangane da wadanda suka karyata rayuwar Lahira suka ce, “Ai rayuwa guda daya ce kawai ta nan duniya. Ba wata rayuwa kuma wacce za mu rayu bayan mun mutu, kuma abin da yake kashe mu dai zamani ne.” Sai Allah Ya ce, “karya suke yi. Ba su da wani dalili a kan wannan magana da suke fada, sai dai zato ne kawai suke yi.” (Jasiya: 24).
An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA) ya ce Annabi (SAW) ya ce, “Allah Yana fada a Hadisin kudsi cewa, “dan Adam yana cutar da Ni saboda zagin zamani da yake yi, alhali kuma Ni ne zamani domin Ni ke kawo dare kuma in kawo wuni.” A wata ruwayar kuma an ce, “Kada ku zagi zamani domin Allah Shi ne zamani.”
Babi na Arba’in da Shida:
Kuskure ne a kira mutum Alkalin Alkalai: An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA), daga Annabi (SAW) ya ce, “Sunan da ya fi kowane muni a wajen Allah shi ne wanda ake ce masa ‘Sarkin Sarakuna’ domin babu wani Sarkin Sarakuna sai Allah.” Sufyanu ya ce, “Mummunan suna a wajen Ubangiji shi ne ‘Alkalin alkalai.” A wata ruwayar kuma an ce, “Sunan da ya fi ba Allah haushi ya kuma fi muni Ranar kiyama shi ne ‘Sarkin Sarakuna.”
Babi na Arba’in da Bakwai:
Girmama Sunayen Allah idan wani ya sanya wa kansa ko dansa sunan Allah to ya canza: An samu Hadisi daga Baban Shuraih, wanda ake kiransa Abul Hakam (wato Baban Hukunci) sai Annabi (SAW), ya ce masa, “Ai wannan sunan Allah ne domin Allah shi ne Mai hukunci kuma gare shi ake mai da hukunci.” Sai ya ce, “Dalilin da ya sa ake kirana da wannan suna, domin idan mutanena suka yi sabani a cikin wani al’amari sai su kawo hukuncin wajena. Idan na yi hukunci sai kowa ya yarda da wannan hukunci. Shi ya sa suke kira na ‘Abal Hakam’. Sai Annabi ya ce, ‘Lallai yin hukuncin abu ne mai kyau amma ba ka kai a ce maka Baban Hukunci ba. Sai Annabi (SAW) ya ce masa, “To kai ba ka da ’ya’ya ne?” Sai ya ce, “Ina da ’ya’ya uku, ina da Shuraihu, ina da Muslim kuma ina da Abdullahi.” Sai Annabi ya ce, “To wane ne babba a cikinsu?” Sai ya ce Shuraihu.” Sai Annabi (SAW) ya ce, to daga yau sunanka Baban Shuraih.” (Abu Dawud ya ruwaito).
Babi na Arba’in da Takwas: Yin izgilanci da sunan Allah ko Alkur’ani ko Manzon Allah kafici ne:
Allah ya ce, “Idan ka tambaye su (Ya Manzon Allah), “Don me kuka yi wannan magana?” Sai su ce, “ai idan muka shiga cikin tafiya mukan yi wasa (shi ya sa muka fadi haka)’. Ka ce yanzu da Allah ko ayoyinsa ko Manzon Allah kuke izgili?” (Taubah: 65).
An samu Hadisi daga Ibn Umar da Muhammad bin Ka’ab da Zaidu bin Aslama da kattadah (RA), suna magana tsakaninsu, Sai wani mutum ya tabo labarin Yakin Tabuka sai ya ce, ‘Ai ba wanda ya fi makarantanmu cin abinci, ba kuma wanda ya fi su karya sannan ga su da tsoro idan aka hadu da abokan gaba. Yana nufin wai Annabi (SAW) ne da sahabbansa su ne makarantan. Nan take sai Aufu dan Malik (RA) ya ce, “karya kake munafiki. Sai na fada wa Annabi (SAW) wannan magana.” Sai Aufu ya tafi wajen Annabi (SAW) domin ya fada masa, sai ya samu Alkur’ani ya rigaye shi. Shi kuma wannan mutum da ya ji haka, sai ya zo wajen Annabi (SAW). Kafin ya zo ya iske Annabi (SAW) har ya hau taguwarsa. Sai ya ce, “Ya Manzon Allah! Mu mun kasance idan mun kutsa cikin tafiya muna hira a tsakaninmu irin hirar matafiya a tsakaninsu domin tafiyar ta yi sauki. Sai Ibn Umar (RA) ya ce. ‘Ina ganinsa lokacin da yake rike da linzamin taguwar Annabi (SAW), tsakuwa suna hawa kafafuwansa.” Sai ya ce, “Ya Rasulallah! Ai mu muna kutsawa cikin tafiya, muna wasa ne.” Sai Annabi (SAW) ya ce masa, “To da Allah ko da ayoyinsa ko da Manzonsa kuke wasa? To kada ku kawo hanzarinku, hakika kun kafirta a bayan imaninku.” Annabi (SAW) ko waiwayowa bai yi ba, kuma bai kara yi masa wata magana ba. (Wannan shi ne dalilin saukar wannan ayar).
DSP Imam Ahmad Adam Kutubi
Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3, Abuja, 08036095723