Tauhidi ginshiqin Musulunci (13)

Babi na Arba’in da Tara:  Butulci ne mantawa da ni’imomin Ubangiji: Allah ya ce, “Idan Muka dandana wa mutum rahama bayan tsanani ya shafe shi sai ya ce, kokarina ne ya fitar da ni daga wahala, ni kuma ba ni zaton za a iya Tashin kiyama. (kuma ko da an yi Tashin kiyama) idan na […]

Tauhidi ginshiqin Musulunci (13)
Tauhidi ginshiqin Musulunci (13)

Babi na Arba’in da Tara:

 Butulci ne mantawa da ni’imomin Ubangiji: Allah ya ce, “Idan Muka dandana wa mutum rahama bayan tsanani ya shafe shi sai ya ce, kokarina ne ya fitar da ni daga wahala, ni kuma ba ni zaton za a iya Tashin kiyama. (kuma ko da an yi Tashin kiyama) idan na koma wajen Ubangijina zan samu kyakkyawan sakamako.” (Sai Allah ya ce) hakika Za mu bai wa kafirai labarin abin da suka aikata kuma Za mu dandana musu azaba mai tsanani.” (Fussilat: 50).

Mujahid ya ce irin wadannan mutanen su ne idan suka samu wata dukiya sai su ce “ai kokarina ne ya ba ni. Ni na cancanta in samu abin!” Ibn Abbas ya ce, “Idan wani alheri ya same shi sai ya ce, “ai daga wajena ne” kamar yadda karuna ya fada da aka ba shi dukiya, maimakon ya ce daga Allah ne, sai ya ce “Ai kwarewata ce ta ba ni ita!” kattada ya ce, “Sai ya ce “Ai ilimina na sanin kasuwanci ne ya ba ni wannan dukiya.” 

Wadansu kuma suka ce, kamar mutum ne ya samu watar dukiya sai ya ce “Ai dalilin wani ilimi ne daga Allah, amma ni ne na fi dacewa a bai wa wannan dukiya.” Wannan ya yi daidai da maganar Mujahid ke nan da ya ce, “Ai an ba ni wannan dukiya ce saboda wata daukaka tawa.”

An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA), Annabi (SAW) ya ce, “An jarraba wadansu mutum uku daga Bani Isra’ila. Mutanen su ne mai ciwon kuturta da mai kora da makaho. Sai Allah ya aiko wa mai ciwon kuturtar nan da Mala’ika cikin siffar mutane. Sai Mala’ikan ya ce wa kuturun, “Me kafi so a rayuwarka?” Sai kuturun ya ce, “Babu abin da na fi kauna kamar launi mai kyau da kuma fata mai kyau. Wannan ciwon kuma da mutane suka guje ni dominsa, a yaye mini shi.” Sai mala’ikan ya shafe shi, nan take sai ya warke, aka ba shi lafiya da launi da fata mai kyau. Sai ya ce masa. “Yanzu wace irin dukiya ka fi so a rayuwarka?” Sai ya ce, “Na fi son taguwa ko saniya.” Mai ruwayar ya yi kokwanto ko wane ne a ciki. To daga karshe dai sai aka ba shi taguwa mai haihuwa ya kuma yi masa addu’a ya ce, “Allah Ya yi wa dukiyarka albarka.”

Shi wannan Mala’ikan sai ya tafi wurin mai kora ya tambaye shi, “Wane irin abu ka fi so a rayuwarka?” Sai ya ce, “Gashi mai kyau. Kuma wannan ciwon da ya same ni ya warke.” Sai ya shafe shi nan take sai ya warke, aka ba shi lafiya da gashi mai kyau. Sai ya tambaye shi, “Wace irin dukiya ka fi so a rayuwarka?” sai ya ce, “Saniya ko taguwa.” Sai aka ba shi saniya mai ciki ya ce, “Allah Ya yi mata albarka.” Sai Mala’ikan ya zo wajen makaho ya ce, “Me ka fi so a rayuwarka? Sai ya ce, “Gani domin in rika ganin mutane da shi.” Sai Mala’ikan ya shafe shi sai ga shi yana gani. Sai ya tambaye shi, “Wace irin dukiya kake so?” Sai ya ce, “awaki.” Sai aka ba shi akuya mai haihuwa.

Sai dukiyoyin kuturun nan da na mai kora suka hayayyafa. Shi na mai akuyar sai ga shi da awaki garke-garke. Na dayan sai ya kansance yana da garke-garke na rakuma, na biyun kuma yana da garke-garke na shanu, na ukun kuma yana da garke-garke na awaki. Sai wannan Mala’ikan ya sake dawowa cikin siffa ta mutanen bayan wasu shekaru. Sai ya zo ga kuturun nan a siffa irin ta kutare sai ya ce masa, “Ni mutum ne miskini kuma ga shi guzurina ya kare kuma garinmu da nisa, ba yadda za a yi in isa garinmu sai da taimakon Allah sannan da taimakonka. Ina rokonka don Wanda Ya ba ka launi mai kyau Ya ba ka fata mai kyau Ya kuma ba ka dukiya ka ba ni taguwa (rakuma) daya in sayar in samu abin guziri.” Sai ya ce, “Kai, ba zan iya ba ka taguwa ba. Ni ma damuwata tana da yawa.” Sai ya ce, “Ai ko kamar na sanka a da, ai kuturu kake kamar yadda nake. Ashe kai ba kuturu ba ne, mutane suna gudunka, kuma kana matalauci Allah ya ba ka dukiya?” Sai ya ce, “Ba ni ba ne. Wannan dukiya na gaje ta ce daga iyaye da kakanni?” Sai ya ce masa, “Idan karya kake Allah Ya mai da kai yadda kake? Sai ya ce “Eh.” sai ya koma kuturu yadda yake da.

Sai Mala’ikan ya tafi wajen mai kora cikin irin siffarsa ta da, ta mai kora, ya fada masa irin abin da ya fada wa wancan mutum na farko. Shi ma mai korar sai ya mayar masa kamar yadda kuturun nan ya amsa masa. Sai ya ce, “Idan karya kake Allah ya mai da ka yadda kake da?” Sai ya ce “Eh.” Sai shi ma ya koma yadda yake.

Sai Mala’ikan ya zo wajen makaho da irin siffar makaho ya ce masa, “Ni mutum ne miskini, matafiyi ga shi kuma guzurina ya yanke min. ba yadda za a yi in kai garinmu a yau sai da taimakon Allah sannan da taimakonka. Ina rokonka domin Wanda Ya mayar maka da ganinka ka ba ni akuya daya in sayar in samu guzurin da zai kai ni garinmu.” Sai ya ce, “Ni ma da makaho nake, sai Allah Ya mayar min da ganina. Wallahi, duk abin da kake so cikin wadannan dabbobi ka dauka, ka bar kuma duk abin da ba ka so. Wallahi ba ni da wata damuwa koda ka kore su duka tunda na ba da su domin Allah ne.” Sai ya ce, “Rike dukiyarka, Allah Ya yi mata albarka. Ku uku Allah ya jarraba amma biyu sun fadi, kai kadai ka ci jarrabawa. Hakika Allah Ya yarda da kai, su kuma abokanka biyu, Allah Ya yi fushi da su.” (Bukhari da Muslim suka ruwaito).

  Babi na Hamsin: 

Butulcewar dan Adam: Allah ya buga misali game da masu rokonSa idan suka shiga wani tsanani. Yayin da aka yaye musu wannan tsananin sai kuma su butulce wa Allah, inda yake cewa, “Lokacin da ya ba su da nagari, sai su sanya wa Allah abokin tarayya cikin abin da Ya ba su. Allah ya daukaka ga barin masu hada shi da wani.”  (A’araf: 190).

Ibn Hazmin ya ce, malamai sun dace a kan duk wani suna da aka dangana da wani ba Allah ba kamar a ce ‘Bawan Amru’ ko ‘Bawan ka’aba’ ko ‘Bawan Kasuwa’ ko ‘Bawan Gona’ da makamantansu. Amma Abdul-Muttalib, suna ne mai kyau. 

Shi kuma Ibn Abbas (RA) cewa ya yi dalilin saukar wannan ayar ta Suratul A’araf shi ne, lokacin da Hauwa’u, matar Annabi Adamu (AS) ta dauki ciki sai Shaidan ya zo musu ya ce, “Ni ne abokinku din nan da na fitar da ku daga Aljanna. Ko dai ku bi ni ko kuma in fitar muku da da mai kaho kuma kahon ya cutar da shi. Idan ba ku bi ni ba, hakika sai na aikata haka (har sau biyu). Idan ba ku son in yi muku haka, ku sanya masa ‘Bawan Gona.” Sai suka ki su bi shi sai dan ya fito matacce. Sai ta sake yin wani cikin, sai Shaidan ya sake zuwa musu kuma ya fada musu irin maganar farko. Su kuma sai suka ki su bi shi, sai wannan dan shi ma ya fito matacce. Sai ta sake daukar ciki na uku, suka ga kamar kin bin sa da suka yi ne ya sa ’ya’yan suke fitowa matattu. Su kuma ga shi suna son da sai suka yarda suka sanya masa suna ‘Bawan Gona.’ Wannan shi ne dalilin saukar wannan aya ta Suratul A’araf. Amma a daya ruwayar ta Ibn Abbas (RA) wacce kattada ya ruwaito cewa ya yi, wato sun yi tarayya ne da Allah wajen biyayya ba wajen bauta ba.

DSP Imam Ahmad Adam Kutubi 

Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3,

Abuja, 08036095723