Tauhidi ginshiqin Musulunci (14)

An sake samun Hadisi daga Ibn Abbas (RA) wanda Mujahid ya ruwaito kan fadin Allah (SWT), “Idan Ka ba mu da nagari za mu zama masu gode maKa. Amma lokacin da Allah ya ba su da nagari sai suka sanya masa abokin tarayya cikin abin da ya ba su. To Allah ya tsarkaka daga abin […]

Tauhidi ginshiqin Musulunci (14)
Tauhidi ginshiqin Musulunci (14)

An sake samun Hadisi daga Ibn Abbas (RA) wanda Mujahid ya ruwaito kan fadin Allah (SWT), “Idan Ka ba mu da nagari za mu zama masu gode maKa. Amma lokacin da Allah ya ba su da nagari sai suka sanya masa abokin tarayya cikin abin da ya ba su. To Allah ya tsarkaka daga abin da ake hada shi da shi.” To sai Hauwa’u da Adamu suka ji tsoro kada dan ya fito ba mutum ba sai suka sanya masa wannan suna (shi ya sa wannan aya ta sauka tana hana sanya wa da sunan bawan wani ba Allah ba).

Babi na Hamsin da daya: Sunayen Ubangiji Kyawawa:

Allah ya ce, “Allah Yana da kyawawan sunaye (idan za ku yi addu’a) ku roke Shi da su. Ka bar wadanda suke canja (kutsawa a cikin) sunan Ubangiji.” (A’araf, 180).

An samo daga Ibn Abbas ya ce, fassarar “Yulhiduna fi asma’ihi ita ce “Suna tarayya da Ubangiji. A wata ruwaya kuma Ibn Abbas (RA) ya ce sunan nan na ‘Ilahu shi ne suka mayar ‘Lata’ kuma sunan Allah na ‘Azizi’ shi ne suka mayar ‘Uzza.’

Shi kuma A’amah ga abin da ya ce, “Suna shigar da wasu abubuwa da babu su cikin sunayen Allah.”

 Babi na Hamsin da Biyu: Ba a cewa ‘Assallamu alallah’:

An samu Hadisi daga lbn Abbas (RA) wanda Mujahid ya ce, mun kasance tare da Annabi (SAW). Idan muka yi sallama bayan Sallah sai mu ce ‘Assalamu alallah (Aminci ya tabbata ga Allah) daga bayinsa, aminci ya tabbata ga wane aminci ya tabbata ga wane.’ Sai Annabi (SAW) ya ce, “Kada ku ce aminci ya tabbata ga Allah domin Shi ne aminci.”

 Babi na Hamsin da Uku: Ba a cewa Allah Ka gafarta mini in Ka ga dama:

An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Kada dayanku ya ce ‘Allah Ka gafarta min in ka ga dama’ ko ‘Allah Ka jikaina in ka gadama.’ Abin da ya sa aka ki haka domin maganar ba ta da ladabi kuma domin ana so mutum ya girmama abin saboda Allah ba ya kin kowa.

An samu Hadisi daga Imam Muslim ya ce, ana son mutum ya nuna girman kwadayinsa ga abin da yake roko domin duk abin da Allah ya bayar ba ya damunSa.

 Babi na Hamsin da Hudu: An yi hani ga cewa ‘bawana ko baiwata’:

An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA) cewa Annabi (SAW) ya ce, “Kada daya daga cikinku ya ce, ‘Ciyar da Ubangijinka’ ko ‘yi wa Ubangijinka tausa.’ Amma kana iya cewa, ‘dana’ ko ’yata’ ko yarona.’ 

Babi na Hamsin da Biyar: Ba a hana wanda ya roki abu domin Allah:

Ibn Umar (RA) ya karbo daga Annabi (SAW) cewa, “Ba a hana duk wanda ya roki abu domin Allah. Wanda kuma ya nemi tsari da ku, to ku tsare shi domin Allah. Wanda kuma ya kira ku, to ku amsa masa (wato wanda ya kira ku domin ku taimaka masa da wani abu). Wanda kuma ya yi muku alheri to kuma ku saka masa.  Idan ba ku samu abin da za ku saka masa da shi ba, to ku yi masa addu’a har ku ga kun saka masa alherin da ya yi muku.” (Abu Dauda ya ruwaito).

 Babi na Hamsin da Shida: Ba a rokon Allah a ce domin fukarSa sai dai idan Aljannah ce:

Jabir (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Ba a rokon komai a ce domin hasken fuskar Ubangiji sai idan abin Aljannah ce.” (Abu Dauda ya ruwaito). (Wato wannan Hadisi yana nuni da cewa babu wani abu da ya kai darajar a roki Allah a ce domin hasken fuskarsa sai Aljannah).

 Babi na Hamsin da Bakwai: Hani ga fadin ‘Da na sani’:

Allah ya ce, (Munafukai) suna cewa, ‘Da a kan gaskiya muke da ba a kashe mu (a Yakin Uhud) ba. Ka ce musu (Ya Muhammad), ko da a gidajenku kuke kwance wadanda Allah yace za su mutu a wuri kaza, to ko ba yakin sai Allah Ya kaddari su fita su je wurin kuma a kashe su din.” (Ali Imran: 154).

Allah ya ce, “Wadanda suka cewa ’yan uwansu kada ku je yaki, su kuma suka zauna a gidajensu suka ki fita yaki (wato ranar Yakin Uhud, da aka dawo yakin sai munafukai suke ce wa Musulmi). Da kun bi abin da muka fada muku da ba a kashe ku ba.” (Ali Imran: 168).

An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA) ya ce Annabi (SAW) ya ce, “Ka yi kwadayin duk wani abin da zai amfane ka amma ka nemi taimako daga Allah kuma kada ka gajiya (wajen nema). Idan wata hasara ta same ka kada ka ce ‘da na aikata kaza da wannan hasara ba ta same ni ba.’ Amma ka ce ‘Haka Allah ya kaddara.’ Allah kuma yana aikata abin da ya so. Domin fadin ‘Da ban yi kaza ba,’ tana bude kofar Shaidan.”

Babi na Hamsin da Takwas: Hani kan zagin iska:

An samu Hadisi daga Ubayyu bin Ka’ab (RA), Annabi (SAW) ya ce, “Kada ku zagi iska amma idan kuka ga abin da kuke ki (idan iska ta taso), to ku ce ‘Allah muna rokonKa alherin wannan iskar da kuma alherin da ke cikinta, da kuma alheri da aka aiko ta da shi. Kuma muna neman tsari daga gare Ka ya Ubangiji! Daga sharrin wannan iska da sharrin da ke cikinta da sharrin da aka umurce ta.” (Imam Tirmizi ya ruwaito).

 Babi na Hamsin da Tara: Mummunan zato ga Allah haramun ne:

Allah ya ce, “(Munafukai) suna mummunan zato ga Allah irin zaton Jahiliyya. Suka ce ‘yanzu muna kan wani abu ne? to ka ce musu (Ya Muhammad) ai al’amari baki daya a hannun Allah yake. Suna boye abin da ba su bayyana maka, suna cewa da muna kan wani al’amari (daga wajen Allah) ai da ba a kashe mu (a Yakin Uhud) ba.’ Ka ce musu (Ya Muhammad) ko da kuna kwance a gidajenku, wadanda Allah ya rubuta musu mutuwa sai sun je inda za a kashe su din. (Wato ko da ba su je yaki ba ke nan). Dalilin da ya sa Allah ya aikata haka domin ya bayyana abin da ke cikin zukatanku ne (na munafunci) kuma domin Allah ya tace abin da ke cikin kirazanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin zukata.” (Ali Imran: 154). 

A wata ayar kuma Allah yana cewa, “Masu mummunan zato ne ga Ubangiji. Kewaye da su ne mummunan zato yake.” (Fathi: 6). Ibn Kayyim ya fassara wannan ayar da cewa, suna zaton Allah ba zai taimaki Manzonsa (SAW) ba ne kuma al’amarinsa zai tozarta ko ya ruguje. Kuma suka fassara cewa abin da ya samu Annabi (SAW) ba daga Allah ba ne ko hikimarSa. An fassara wannan kuma da musanta hikimar Ubangiji da kaddara da kuma musanta cewa sakon da aka bai wa Annabi ba zai iya isar da shi ba da kuma cewa Allah ba zai dora Musulunci a kan sauran addinai ba. To wannan shi ne mummunan zaton da mushrikai da munafukai suka yi wa Allah a cikin Suratul Fathi. 

Abin da ya sa aka ce wannan mummunan zato ne, saboda bai dace a jingina shi ga Allah ba, ko hikimarsa, ko gode masa da kuma alkwarinsa na gaskiya. Domin duk wanda ya yi zaton za a dora karya a kan gaskiya, kuma ta tabbata har ma ba za a iya gane gaskiyar ba, ko ya musanta cewa abin da ya faru ba da sanin Allah ko kaddarawarsa ba ne, ko ya musanta ikon Ubangiji bisa ga hikima ce wacce ta cancanci godiya, ko suka yi zaton cewa ta zo ne daga tsantsar nufinsa, to wannan shi ne zaton kafirai. To azabar wuta ta tabbata ga kafirai. Mafi yawan mutane suna yi wa Allah mummunan zato cikin abin da ya kebanta da su ko abin da ya aikata ga wasunsu. To ba wanda zai yarda da cewa duk abin da ya same shi daga Allah ne, sai wanda ya san Allah da sunayensa da sifoffinsa wanda hikimarsa tana iya tabbatar da haka da kuma gode masa a kan haka. 

 DSP Imam Ahmad Adam Kutubi 

Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3,

Abuja, 08036095723