Tauhidi ginshiqin Musulunci (8)
Babi na Ashirin da Biyar Nau’o’in sihiri Imam Ahmad ya samu Hadisi daga Muhammad xan Ja’afar (RA) shi kuma daga Hayyanu xan A’la’i daga Qutnu xan Qabisatu daga Babansa ya ji Annabi (SAW) yana cewa: “Kukan tsuntsu da ake camfi da shi da kuma zane da ake yi a qasa domin duba da kururuwan lbilis […]
Babi na Ashirin da Biyar
Nau’o’in sihiri
Imam Ahmad ya samu Hadisi daga Muhammad xan Ja’afar (RA) shi kuma daga Hayyanu xan A’la’i daga Qutnu xan Qabisatu daga Babansa ya ji Annabi (SAW) yana cewa: “Kukan tsuntsu da ake camfi da shi da kuma zane da ake yi a qasa domin duba da kururuwan lbilis dukansu sihiri ne.” Shi kuma Autu ya ce iyyafatu’ kukan tsuntsu ne kamar kukan mujiya. Ya ce “Darq” kuma zane ne da ake yi a qasa domin duba. Shi kuma ‘Jibtu,’ Hassan ya ce kururuwar lbilis ne. (an samu wannan fassara ne daga Abu Dawud da Nisa’i da Ibn Hibban).
Ibn Abbas ya ce, “Duk wanda ya nemi ilimin taurari domin ya yi duba da su, to ya yi sihiri, koyaushe ya qara neman ilimin taurari, ya qara shiga cikin sihiri ne.” (Abu Dawud ya ruwaito).
Imam Nisa’i ya ruwaito daga Abu Huraira (RA) cewa: “Duk wanda ya qulla wani qulli ya yi tofi a cikinsa, to, haqiqa ya yi sihiri. Wanda kuma ya yi sihiri to ya yi shirka. Wanda ya rataya wani abu a wuyansa, to za a rataya imaninsa a kan wannan abin.” Amma a ruwayar Ibn Mas’ud (RA) ga yadda Annabi (SAW) ya ce, “Kuna so in faxa muku ko mene ne ‘Adah?’ Shi ne annamimanci, shi ne haxa mutane biyu rigima. Imam Bukhari da Muslim suka ruwaito. A sigar wani Hadisi da Bukhari da Muslim suka ruwaito, Annabi (SAW) ya ce, “Wani sashen bayani sihiri ne.”
Babi na Ashirin da Shida
Bokanci
An samu Hadisi daga Imam Muslim daga waxansu daga cikin matan Annabi (SAW) sun ce, Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya je wurin boka ya tambaye shi wani abu, ya bayyana masa kuma ya gaskata shi, to ba za a karvi sallarsa ta kwana arba’in ba.”
An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya je wajen boka har ya gaskata shi a kan abin da ya faxa, to ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad (SAW).” Abu Dawud ya ruwaito.
An samu Hadisi daga mutum huxu waxanda Hakim ne na biyar xinsu, kuma sun ce wannan Hadisi ya zo ne a sharaxin Bukhari da Muslim: “Wanda ya je wajen xan duba ko boka ya gaskata shi, to haqiqa ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad (SAW).” Shi kuma Abu Ya’ala ya ji daga Ibn Mas’ud (RA) misalin wannan Hadisi da Abu Hakim ya ruwaito. Amma Imrana xan Hussaini ya ce, Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yi camfi ko aka yi masa camfi ba ya tare da ni, ko ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci, ko ya yi sihiri ko aka yi masa sihiri. Sannan duk wanda ya je wajen boka ya gaskata abin da ya faxa, to haqiqa ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi (SAW).” Bazzar ne ya ruwaito. Imam Xabrani ya ce, wannan Hadisi na Imrana xan Husaini, sahihi ne domin Ibn Abbas (RA) ya ruwaito shi amma ban da “wanda ya je wajen xan duba ………” har zuwa qarshen Hadisin.
Imam Bagwi ya fassara “Arraf’ da wanda ya ce ya san abin da aka sace da wanda ya saci abin da wajen da aka yi satar da inda kayan satar suke da makamantansu. A wata ruwayar abin da ake kira ‘Arraf’ shi ne boka. Shi kuma boka sh ine wanda ke ba da labarin gaibi, kamar abin da zai faru gobe ko abin da zai faru nan da mako guda ko wata xaya ko shekara xaya. A wata ruwayar kuma an ce shi ne wanda zai ba ka labarin abin da ke cikin zuciyarka.
Shaihul Islam Ibn Taimiyya cewa ya yi da boka da xan duba duk xaya ne domin xan duba shi ne boka, shi kuma boka shi ne mai duba da taurari ko da qasa ko da tattabara ko da qwai ko da wuri ko da tasbaha da makamantansu. Shi ne wanda ke ba da labarin abin da zai faru nan gaba ta waxannan hanyoyi.
Ibn Abbas (RA) ya ce, akwai waxansu mutane da suke duba da alifun, ba’un da ta’un. Da waxannan ne suke duba zuwa ga taurari domin su yi bokanci. Ibn Abbas ya ce, wanda ya aikata wannan ba ya da rabo a wurin Allah.
Babi na Ashirin da Bakwai
Warware sihiri ga wanda aka yi wa sihiri
Jabir (RA) ya ce, an tambayi Annabi (SAW) a kan hukuncin warware sihiri ga wanda aka yi wa sihiri sai Annabi (SAW) ya ce, “Yin haka aikin Shaixan ne.” Ahmad da aka tambaye shi sai ya ce, Ibn Mas’ud ya ce yin haka makruhi ne. Shi kuma Qattadatu ya tambayi xan Musayyib, mutum ne aka yi masa sihiri ba ya iya saduwa da matarsa, shin ya halatta a yi masa abin da zai warware wannan sihirin? Ya ce, yin haka idan ba sihiri ba ne ba laifi, domin abin da ake nema shi ne gyara. Tunda gyara ake nema duk abin da zai amfanar babu laifi idan dai ba sihiri a cikinsa. Shi kuma Hassan ya ce, ba wanda zai iya warware sihiri sai idan shi ma mai sihiri ne. Imam Ibn Qayyim ya ce, abin da ake nufi da ‘nushrah’ shi ne a warware sihiri ga wanda aka yi wa sihirin. Yin haka kuma ya kasu kashi biyu. Na xaya a warware sihiri da sihiri irinsa. To wannan shi ne aikin shaixanun malamai. Wannan ya yi daidai da maganar Hussan da ya ce, ba mai warware sihiri sai mai sihiri. Ta wannan hanyar, sai mai warware sihirin ya kusantar da wanda aka yi wa sihirin ga Shaixan, sai ya warware sihirin ga wanda aka yi wa sihirin. Na biyu kuma shi ne warware sihiri ga wanda aka yi wa sihiri da addu’o’i da magunguna da sauransu. To wannan ya halatta.
Babi na Ashirin da Takwas
Camfe-Camfe
Lokacin da Annabi Musa (AS) ya zo mutanensa sun camfa shi. Suka ce an qi yin ruwa, sun shiga cikin talauci da cututtuka. Suka ce shi ne ya yi dalilin shigarsu wannan hali. Shi ne Allah (SWT) yake faxa a cikin Suratul A’araf cewa: “Waxannan halayen da suke ciki daga wajen Allah ne (ba wai domin zuwan Musa ba ne). Sai dai mafi yawansu ba su gane haka ba.” (A’araf:131). A wata ayar kuma sai Allah ya ba su amsa da cewa: “Wahalolinku, ku kuka jawo wa kanku. Don kawai an yi muku wa’azi sai ku camfa mai wa’azi? Lallai ku mutane ne masu varna.” (Yasin, 19).
Abu Huraira ya ce Annabi (SAW) ya kore waxannan abubuwa guda huxu da mutane ke camfawa. Babu tashin ciwo daga wajen wani zuwa ga wani, babu camfi, babu cewa idan mujiya ta yi kuka wani zai mutu, babu kuma cewa ba a tafiya ko aure a cikin watan safar. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Sai dai Imam Muslim ya qara biyu a ruwayarsa, bakan-gizo da ke fitowa a ce ya shanye ruwa domin haka ba za a yi ruwa ba, ba haka ba ne, kuma wani aljani da ake kira Ra’asul Goul mai vatar da mutane shi ma Annabi (SAW) ya ce ba gaskiya ba ne.
A wani Hadisi da Anas ya ruwaito ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Ba wani ciwo da zai tashi da kansa daga jikin wani ya harbi wani, kuma camfi ba ya da kyau.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Fa’lu yana yi min daxi”. Sai sahabbai suka ce, mene ne ‘Fa’lu sai Annabi (SAW) ya ce, “Magana ma kyau wacce ba camfi ba.”
DSP Imam Ahmad Adam Kutubi
Zone 7 Police Headquaters Wuse Zone 3, Abuja, 08036095723