Taurarin Zamani: Umar Farouk (Shakaka)

Shakaka ya ja hankalin matasa cewa harkar siyasa ba sana’a ba ce.

Taurarin Zamani: Umar Farouk (Shakaka)

Shakaka

Shakaka ya bayyana yadda rashin aikin yi da tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya suka sa ya kafa kamfanin daukar hoto domin dogaro da kansa.

Kazalika, ya shaida wa shirin Taurarin Zamani na Aminiya yadda ya dinga tara kudin da ake ba shi na NYSC har ya sayi kyamarar da ya fara aiki da ita.

Har wa yau, ya bayyana yadda ya kasa barci sakamakon ƙonewar hotunan wani biki da ya taba dauka.

Matashin ya ce Soshiyal Midiya ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar kamfaninsa na daukar hoto, domin yawancin kwastomominsa daga Soshiyal Midiya suke.

Shakaka ya ja hankalin matasa cewa harkar siyasa ba sana’a ba ce, yana da kyau kowa ya samu sana’ar dogaro da kai duba da yadda al’amura suka lalace a kasar nan.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos