Taurarin Zamani: Zikirullahi Alaka
Ya ce duk da haka, kada abokan sana’arsa su damu da irin kallon da ake musu na masu bata tarbiyya.
![Taurarin Zamani: Zikirullahi Alaka Taurarin Zamani: Zikirullahi Alaka](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/02/Screenshot_2024-02-14-20-56-09-789_com.instagram.android-edit.jpg)
Jarumin Kannywood Zikirullahi Abubakar ya bayyana wa shirin Taurarin Zamani na Aminiya damuwarsa kan yadda wasu ke wa ‘yan masana’antar kallon jahilai.
Game da zargin bata tarbiyya a Kannywood kuwa, Zikirullahi ya ce wadanda ake gani a haka, da ma tun daga gidan iyayensu a lalcensu suke, don haka ba a masana’antar suka lalace ba.
Amma ya ce duk da haka, kada abokan sana’arsa su damu da irin kallon da ake musu na masu bata tarbiyya.