Tauraruwa Mai Wutsiya
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Muhamadu Buhari da ya mayar da hankali kan batun sake fasalta Najeriya, daidai da ra’ayin da ‘yan kungiyar NADECO da Afenifere na yankin Kudu-maso-Yammacin kasar nan suka dade suna da’awarsa. A takaice dai Alhaji Atiku Abubakar na bukata a yi wadansu al’amura don inganta tsarin […]
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Muhamadu Buhari da ya mayar da hankali kan batun sake fasalta Najeriya, daidai da ra’ayin da ‘yan kungiyar NADECO da Afenifere na yankin Kudu-maso-Yammacin kasar nan suka dade suna da’awarsa. A takaice dai Alhaji Atiku Abubakar na bukata a yi wadansu al’amura don inganta tsarin federaliyya, ko kuma na zaman tarayya, a daidai wannan lokacin da hankulan ‘yan Najeriya ya raja’a ga yadda za a kawar da rashawar da ta hana kasar kumari da kuma karfafa yanayin tsaro don a samu lumana da zaman lafiyar da za su wanzar da ci gaba da karuwar arziki.
Da farko dai Atiku Abubakar na so a ragewa gwamnatin tarayya karfi, a kuma kara karfafa gwamnatocin jihohi; na biyu kuma yana so a yi zaman tarayya na ci-naka-in-ci-nawa, ko kuma a ce kowa ya kamo kifi ya jefa a cikin gorarsa, watau abin da ‘yan Kudu ke kira Resource Control, ko kuma Fiscal Federalism; sa’annan kuma yana so a yi zaman da zai ba kowane bangaren kasar nan damar tsarawa ko kuma kago wani al’amarin da ya dace da manufar jama’arsa da kuma bukatunsu da suka sha-bamban da na sauran sassan kasar nan, abin da a Turance ‘yan Kudu ke kira True Federalism. A karkashin wannan tsarin bangarororin kasar nan na iya bullo da ‘yan sandan jihohi da kuma yadda za su yi hulda ko mu’amala da sauran sassan Tarayyar Jamhuriyar Najeriya.
Wasu ‘yan Najeriya dai sun riga Alhaji Atiku Abubakar yin kiraye-kiraye don a gabatar da wannan shawara tasa, domin a ganinsu yin haka zai sa kowane bangaren kasar nan farkawa daga barci, ya kuma tashi ya nemi na kansa, ko kuma ya cire wa kansa kitse a wuta. Ta haka ne kuma jama’ar kowane gefen kasar za su tabuka wajen rayawa da inganta shi, ko kuma su shantake, a tafi a bar su a banza. A wajen wasu kuma hakan ba shi ne mafita ba don warkar da matsalolin da suka dade suna fama da su ba, musamman ma na koma-baya da tashe-tashen hankula da matsalolin tattalin arziki. A bisa gaskiya babu wani sabon tsarin da ake ce-ce-ku-ce akai, wanda zai dore a kasar nan ba tare da ingantaccen shugabanci ba. Halin da shiyyar Kudu- maso-kudu ta shiga ya isa ishara game da yadda ita da sauran shiyyoyi ke fama da wahalhalu, ba domin komai ne ba kuwa sai don rashin ingantaccen shugabancin da zai sarrafa albarkatun da ake da su don biyan bukatun kowa da kowa.
A yanzu kuma sai ga shi nan ‘yan ta’addan yankin Neja Dalta sun sake taso da batutuwan tsare-tsare domin gyara Najeriya, ciki kuwa har da cin-gashin-kai da kuma ci-naka-in-ci nawa, watau “True Fedrealism da kuma Fiscal Federalism,” a daidai lokacin da Alhaji Atiku Abubakar ke bayar da shawara don aiwatar da irin wadancan bukatun na ‘yan Kudu , wadanda ‘yan Najeriya suka sanya kafafu, suka shure da dadewa. Ko a ranar Lahadin da ta gabata ma sai da wasu fitattun ‘yan adawa daga yankunan Gabashi da Yammacin kasar nan, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Chief Aled Ekweme da tsohon Ministan Yada labarai, Farfesa Jerry Gana da tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Chief Chukwuemeka Ezeife da kuma wani jigo a tsohuwar kungiyar NADECO, Ayo Adebanjo suka yi kira ga Shugaba Muhamadu Buhari da ya sake tsarin Najeriya, yadda al’amura da harkokinta za su dace da manufar da suka dade suna da’awarta
Wadannan mutanen, da kuma wadanda suka yi jawabai a wajen wani taro da aka yi a karo na 17 na kungiyar matasan ‘yan kabilar Ibo a Enugu, ranar Lahadin da ta gabata, sun bukaci Shugaba Buhari da ya gaggauta amfani da rahoton Babban Taron kasa da tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya sanya a yi a shekarar 2014, don sake tsara yanayin gudanar da al’amura a kasar nan. A takaice dai abin da suke bukata shi ne mayar da Najeriya bisa tafarkin jihohi uku da ake da su kafin samun ‘yanci da kuma kai wa matsayin jamhuriya a 1963.
To Amma Shugaba Buhari ya nuna cewa wannan batu na sake fasalta yanayin kasar nan ba shi cikin alkawuran da ya yi wa jama’a, haka nan kuma babu shi cikin manufofin jam’iyyarsa. Ya kuma ce shi bai ga dalilin da zai sa ya waiwayi wancan rahoton da Gwamnatin Jonathan ta kashe sama da Naira miliyan dubu tara akai ba, kuma ‘yan Najeriya ba su amince da sakamakonsa ba.
A takaice dai ana iya cewa batun tayar da maganar sake fasalin kasar nan da kuma yin amfani da wancan rahoton na babban taron da aka yi a bara waccan wasu sababbin matakai ne da ake son bi don takura Gwamnatin Buhari har a kai ga tayar da zaune tsaye, ta yadda muhimman ayyukan da ya sanya a gaba na tserar da kasar daga kangin wahalhalun da take ciki a halin yanzu za su sha ruwa. Wannan wata dabara ce da aka dade ana amfani da ita wajen takura wa shugabannin kasar nan don yin abin da ba shi ne ke gabansu ba, ana tsorata su da batun sake fasalin Najeriya , don su kidime, su yi abin da makiya kasar ke bukata. Haka aka yi wa marigayi Sani Abacha, kuma wadanda ke kan gaba ne a yanzu wajen nuna wannan bukatar suka yi ta takun-saka da shi kafin ta Allah ta kasance a kansa. Shi ma Goodluck Jonathan ba shi da ra’ayin sake fasalta kasar, amma haka nan aka kuntata masa kiran taron da ake gani zai share fagen yin haka kusan karshen wa’adinsa a shekarar 2014, an kuma yi, amma taron bai tsinana komai ba don an gano kokarin wasu na biye son zukatansu don biyan wata mummunar bukatarsu.
To, dangane da haka ne tsohon shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya tayar da wata magana game da Shugaba Buhari, wacce take nuna alamun cewa ana so ne shi ma a takura masa, a gigita shi don ya amince da amfani da wancan rahoton da aka shirya bisa son zuciya, don a tsara sabuwar manufar da za ta kai ga wargajewar Najeriya. A cewar Alhaji Atiku, Shugaba Buhari bai yi la’akari da matsalolin tattalin arzikin da suka dade suna addabar kasar ba, kuma ga shi nan ya samu mulki amma ya rasa yadda zai yi da shi. Wadannan kalamai dai ba za su razana Shugaba Buhari ba har ya kai ga daukar matakan aiwatar da abin da ‘yan Najeriya suka rigaya suka wancakalar.
Yanzu da yake an dawo da wadannan batutuwan, kuma a daidai lokacin da ’yan kabilar Ibo da kuma ‘yan kabilar Ijaw ke dagewa kan ballewa daga tarayyar Najeriya, ana iya cewa da gangan ne domin a tabbatar da cewa an matsa lamba wajen wargajewar Najeriya kamar yadda kasar Amurka da kawayenta suka dade suna fatan afkuwar haka, amma fa sai idan masu hankoron ballewar sun samu dama. To kada a kuskura a ba su.