Taurin bashi: An yanke wutar gidan gwamnati da ma’aikatu 51 a Taraba

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki da ke Yola ya yanke wutar lantarki na gidan gwamnatin Jihar Taraba da ke Jalingo saboda gwamnatin ta kasa biyan kudin wuta har Naira miliyan 60. Kamfanin kuma ya yanke wutar lantarki a Babban Asibitin Jalingo da wasu ma’aikatun gwamnati 52. Manajan yanki na kamfanin da ke Jalingo Mista Hanawa […]

Taurin bashi: An yanke wutar gidan gwamnati da ma’aikatu 51 a Taraba
Taurin bashi: An yanke wutar gidan gwamnati da ma’aikatu 51 a Taraba

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki da ke Yola ya yanke wutar lantarki na gidan gwamnatin Jihar Taraba da ke Jalingo saboda gwamnatin ta kasa biyan kudin wuta har Naira miliyan 60. Kamfanin kuma ya yanke wutar lantarki a Babban Asibitin Jalingo da wasu ma’aikatun gwamnati 52.

Manajan yanki na kamfanin da ke Jalingo Mista Hanawa Rufus ya ce amma yanzu an maida wutar bayan Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Sani Abubakar danladi ya roki kamfanin ya maida wutar tare da alkawarin gwamnati za ta biya kudin wutar a cikin kankanen lokaci.
Manajan ya ce kamfanin na bin gwamnatin Jihar Taraba kudin wutar lantarki na tsawon wata hudu, kuma gwamnatin ta nemi a maida wutar lantarki ne don bai wa hukumomin damar gudanar da ayyukansu.
Ya ce Mukaddashin Gwamnan da kansa ya yi alkawarin za a biya kudin kuma saboda haka ne Babban Jami’in Kamfanin da ke Yola ya zo Jalingo aka amince kan yarjejeniyar bayan kudin.
Ya kara da cewa har yanzu gwamnatin ba ta biya kudin ba duk da kasancewar ranar da aka amince cewa za a biya kudin ta wuce. “Saboda girman da kamfanin ke ba gwamnatin ya sa aka kara mata mako daya don haka muna fata gwamnatin za ta cika alkawarinta na biyan kudin don gudun sake yanke wa ma’aikatunta wutar lantarki,” inji Manajan.
Mista Hanawa ya ce kamfanin ya dogara ne kan kudin da masu amfani da wuta ke biya don tafiyar da ayyukansa. Saboda haka ya nemi masu amfani da wutar lantarki su rika biyan kudin wuta a kan lokaci.