Tawagar ECOWAS ta gana da Bazoum
Bazoum ya fada mana matsalolin da yake fuskanta.
Tawagar Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS, ta samu nasarar ganawa da hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum.
Gidan Talabijin na France 24 ya ruwaito cewa, an gudanar da ganawar ce a gaban Firaministan kasar da sojojin da suka yi juyin mulki suka nada, Ali Mahaman Lamine Zeine.
- Tawagar ECOWAS ta koma Nijar domin tattaunawa da sojin da suka hambarar da Bazoum
- ’Yan bindiga sun harbe mai fafutikar kare hakkin bakar fata a Brazil
Da yake zantawa da manema labarai bayana ganaawar, jagoran tawagar, tsohon Shugaban Najeriya na mulkin soji, Janar Abdussalami Abubakar, ya ce hambararren shugaban ya fada musu ’yan matsalolin da yake fuskanta a yayin da yake ci gaba da shan daurin talala.
A yayin da Janar Abdussalami bai yi wani karin haske a kan hakan ba, sai dai ya ce an samu ci gaba dangane da kokarin sulhu da ECOWAS ke yi kan dambarwar siyasa da ta yi wa Jamhuriyyar Nijar dabaibayi.
Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdussalami na kuma dauke da mai alfarma Sarkin Musulmin kasar, Muhammad Sa’ad Abubakar tare da wasu jami’an ECOWAS.
Ana iya tuna cewa, a ziyarar farko da tawagar ta kai kasar a cikin wannan wata, sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ki basu damar ganawa da Bazoum.
To sai dai nasarar ganawar a yanzu, ita ce ta biyu da wata tawaga ta yi da shi, tun bayan hambarar da gwamnatinsa da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan da ya gabata.
Komawar tawagar na zuwa ne kwana ɗaya bayan ECOWAS ta ce taron manyan hafsoshinta na kwana biyu a birnin Accra ya saka ranar kai yaƙi Nijar.
Kwamishinan harkokin siyasa na ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah ya ambato su, suna cewa: “Mun shirya shiga a duk lokacin da aka ba mu umarni.”
Amma dai, ECOWAS ta jaddada cewa duk da wancan mataki ƙofofin sulhunta rikici ta hanyar diflomasiyya za su ci gaba da kasancewa a buɗe.
A ziyarar da malaman addinin Islama daga Najeriya suka kai a makon jiya, a karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau, sojojin sun bayyana musu aniyar tattaunawa da ECOWAS da kuma bukatar ganin an cirewa kasar takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakaba wa Nijar.