Tawagar ECOWAS ta koma Nijar domin tattaunawa da sojin da suka hambarar da Bazoum
Ita ce ziyara ta biyu bayan wadda tawagar ta kai a baya, wanda shugaban sojin yaki karbar su.
Tawagar shiga tsakani na Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta isa Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin ganin an shawo kan dambarwar siyasar ƙasar ta hanyar lumana.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Abdulsalami Abubakar na kuma dauke da mai alfarma Sarkin Musulmin kasar, Muhammad Sa’ad Abubakar tare da wasu jami’an ECOWAS.
- ’Yan bindiga sun harbe mai fafutikar kare hakkin bakar fata a Brazil
- Matsin rayuwa ya sa Magidanci rataye kansa a Jigawa
Tun bayan saukarta a filin jirgin saman Yammai, tawagar ta samu tarba daga Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, wanda sojoji suka naɗa.
Ana sa ran za su tattauna da jagoran mulkin soja, Janar Abdourahmane Tchiani, game da yadda za a mayar da mulki ga farar hula.
ECOWAS ta dage don ganin sojojin su mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki, wanda suke tsare da shi tun 25 ga watan Yuli.
Wannan ce ziyara ta biyu da wannan tawaga ta kai Nijar, bayan wadda ta kai a baya, wanda shugaban sojin yaki karbar su.
Komawar kwamitin na zuwa ne kwana ɗaya bayan ECOWAS ta ce taron manyan hafsoshinta na kwana biyu a birnin Accra ya saka ranar kai yaƙi Nijar.
Kwamishinan harkokin siyasa na ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah ya ambato su, suna cewa: “Mun shirya shiga a duk lokacin da aka ba mu umarni.”
Amma dai, ECOWAS ta jaddada cewa duk da wancan mataki ƙofofin sulhunta rikici ta hanyar diflomasiyya za su ci gaba da kasancewa a buɗe.
A ziyarar da malaman addinin Islama daga Najeriya suka kai a makon jiya, a karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau, sojojin sun bayyana musu aniyar tattaunawa da ECOWAS da kuma bukatar ganin an cirewa kasar takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakaba wa Nijar.