Tawagar neman takarar dan majalisar Kubau ta isa Kalaba

A makon da ya wuce ne, Tawagar ’yan asalin karamar Hukumar Kubau, Jihar Kaduna, karkasin jagorancin Hajiya Binta Garba Ancau suka ziyarci wasu daga cikin jihohin Kudu maso Kudu, domin jawo ra’ayin su, su nemi Alhajin Nasiru Aliyu Damau ya fito takarar mukamin majalisar dokokin Jihar Kaduna. Bayan da ta gana da ’yan asalin karamar […]

Tawagar neman takarar dan majalisar Kubau ta isa Kalaba
Tawagar neman takarar dan majalisar Kubau ta isa Kalaba

A makon da ya wuce ne, Tawagar ’yan asalin karamar Hukumar Kubau, Jihar Kaduna, karkasin jagorancin Hajiya Binta Garba Ancau suka ziyarci wasu daga cikin jihohin Kudu maso Kudu, domin jawo ra’ayin su, su nemi Alhajin Nasiru Aliyu Damau ya fito takarar mukamin majalisar dokokin Jihar Kaduna.

Bayan da ta gana da ’yan asalin karamar hukumar Kubau mazauna Jihar Kuros Riba, a garin Kalaba Aminiya ta nemi Hajiya Binta Ancau ta bayyana makasudin zuwan su kalaba, da ma dalilan su na yin kira ga ’yan uwansu, sai ta ce “ a gaskiya mu al’ummar karamar Hukumar Kubau mun tsaya mun yi lissafin irin ayyukan ci gaba da kuma irin taimakon da yake yi wa jama’a babu babba, babu yaro, ba tare da nuna wani banbanci ba, matukar aka kai masa kuka zai share wa mutum hawayensa, shi ne yasamuka yi tunani wace hanya ce za mu saka wa wannan bawan Allah, sai muka yanke shawarar ai gara mu fara tuntubar ’yan uwa da abokan arziki, mu nemi shawara, mu ce ya fito takara, mu kuma mu mayar masa da buktarsu,”inji ta.
Yar siyasar ta ce, shi mutum ne haziki domin ya taba zama shugaban karamar hukuma, ya yi aikin da talakawa suka ji dadi, shi yasa yanzu da ya zama kwamishina muke rokonsa da ya amsa kiran mu, ya fito takarar majalisar Jihar Kaduna karkashin jami’iyyar PDP. Za mu rufa masa baya”.
Da yake yin karin haske game da lamarin ,mai masaukin bakin, Alhaji Jamilu Ali bayyana farin cikinsa ya yi da jin irin namijin kokari da Alhaji Nasiru Aliyu Damau ke yi
“Idan da ana samun mutane masu taimaka wa talakawa irinsa ai da babu abin da zai sanya matasa na barin gida suna zuwa neman kudi Kudanci kasar nan, tunda an samu wannan hazikin dan siyasa za mu ba shi goyon baya dari-bisa dari, tare da yi masa addu’a Allah ya cika masa buri,” in ji shi.