Tawagar neman takarar shugabancin kasa ga Kwankwaso ta isa Kalaba

Tawagar da ke goyon bayan jama’a su bukaci   gwamnan Jihar Kano, Injiniya Dokta  Rabi’u Musa Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban kasa a jamiyyar APC a zaben 2015, karkashin jagorancin  Alhaji Ahmed Garba  Bichi, ta yi dirar mikiya garin Kalaba fadar Gwamnatin Jihar Kuros Riba .Alhaji Ahmed Garba Bichi  da tawagarsa, wadda ba tare da wani […]

Tawagar neman takarar shugabancin kasa ga Kwankwaso ta isa Kalaba
Tawagar neman takarar shugabancin kasa ga Kwankwaso ta isa Kalaba

Tawagar da ke goyon bayan jama’a su bukaci   gwamnan Jihar Kano, Injiniya Dokta  Rabi’u Musa Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban kasa a jamiyyar APC a zaben 2015, karkashin jagorancin  Alhaji Ahmed Garba  Bichi, ta yi dirar mikiya garin Kalaba fadar Gwamnatin Jihar Kuros Riba .
Alhaji Ahmed Garba Bichi  da tawagarsa, wadda ba tare da wani jinkiri ba suka mika  sakon da suke tafe da shi a bainar jama’ar da ke wurin  gaban Alhaji salisu Abba Lawal sarkin Hausawan Kalaba .
kwamared mohammed Jalal  ne ya gabatar da ’yan tawaga ga Sarkin Hausawan.Ahmed Garba Bichi ya bayyana wa dandazon jama’a makasudun zuwan su jihar kamar haka “ kowa yasan halin da Najeriya take ciki ba sai anfadawa kowa ba ita Nijeriya kowa ya sani kamar yadda ake cewa jiki magayi ,mu kan da muke Jihar Kano da ku kanku da kuke zaune a nan, idan wata hidima ta kaiku jihar da ma makwabtan jihohi da suke kusa da Kano a tsawon shekara uku da rabi Allah ya ba mu gwamna Kwankwaso , duk wanda ya san Jihar Kano shekara hudu da suka  wuce, kafin Allah ya  kawo mana wannan bawan Allah  ya shiga sauran kananan hukumomi da birni ya keta ayyukan raya kasa, ba sai an fada wa mutum ba, za a san cewa hakika an samu ci gaba gagarumi”.inji shi .
Shugaban tuntubar Kwankwaso ya fito takarar 2015, ya kara da cewa lallai yasan akwai abokan sana’a, wato ’yan takara daga sauran jam’iyyu tun da ake zaune kasa daya, muna bukatar kowanen ku ya zama wakili jakadan injiniya Rabi’u musa Kwankwaso a wannna jiha
Alhaji Salisu Abba Lawal Sarkin Hausan Kalaba ya bayyana matukar farin cikinsa game da wannan kira da ake yi wa Gwamnan Kano, tare da yi masa addu’a Allah ya cika muradi.
Sarkin Hausawan ya nuna matukar jin dadinsa da ziyarar neman goyon bayan da aka kawo musu. Sauran ’yan tawagar sun hada da Honarabul Alasan Ado Doguwa dan majalisar wakilai da Mohammed Jalal, da Honarabul Yahaya Adamu Garin Ali, da Alhaji Sule Shuwaki ne suka rufa wa Alhaji Ahmed Garba Bichi baya a ziyarar .