Tawagar Shugaban Kasa ta halarci jana’izar Sani Buhari a Kano
Buhari ya ce jaruman maza irinsu Sani Buhari sun samu nasara ta hanyar jajircewa da aiki tukuru.
Wata tawaga ta Shugaban Kasa ta halarci jana’izar daya daga cikin fitattun ’yan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Sani Buhari Daura da ya riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar.
Tawagar karkashin jagorancin Ministan Sharia kuma Lauyan Koli na Najeriya, Abubakar Malami, ta mika sakon ta’aziyyar ga Mutanen Kano ta hannun Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma iyalan mamacin da ke zaune a Unguwar ’Yar Mai Shinkafi da ke birnin Dabo.
A cikin wasikar da Malami ya mika wa Sarkin Kano a Talatar da ta gabata, Buhari ya ce marigayin ya kasance daya daga cikin manyan yan kasuwa na farko a kasar da suka bayar da gudunmuwa wajen bunkasa tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi ga daruwuwan jama’a.
A wasikar, “Buhari ya ce jaruman maza irinsu Sani Buhari sun samu nasara ta hanyar jajircewa da aiki tukuru.
“Rayuwar marigayi Sani Buhari cike take ta ban kaye domin ta nuna mana cewa tabbas ta hanyar jajircewa da aiki tukuru ana iya samun nasara.
“Ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalansa na Daura da na Kano, da kuma Gwamnatin Jihohin Katsina da Kano. Allah Ya ba ku hakurin jure wannan rashi.
Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar Shugaban Kasar ta samu tarba daga Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da kuma Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Adao Bayero.
Tawagar ta kunshi Ministan Maaikatar Sufurin JIragen Sama, Hadi Sirika, da na Maaikatar Albarkatun Ruwa, Sulaiman Adamu da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu da kuma Mataimakin Babban Jami’in Tsaro na Fadar Shugaban Kasa, Maikano Abdullahi.
Hamshakin dan kasuwar wanda kafin rasuwarsa shi ne mai rike da rawanin Walin Daura, ya bar duniya yana da shekara 89.
Mukasantansa sun shaida wa manema labarai cewa Alhaji Daura ya rasu a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Tun a karshen makon da ya gabata ne iyalansa suka sanar da fara shirye-shiryen dawo da gawarsa nan gida Najeriya domin sanya ta a makwancin karshe.
Bajimin dan kasuwar wanda aka haifa a watan Janairun 1932, shi ne mamallakin Kamfanin gine-gine na Standard Construction Company Limited kuma shi ne ya samar da rukunin kamfanonin Bayajidda.