Tawaye A Majalisun Tarayya: Ya kamata talakawa su fara daukar mataki
Har yanzu talakawan Najeriya ba su gama fita daga daurewar kai game da abin da ya faru ko yake ma cikin faruwa a majalisar kasa ba, inda kiri-da-muzu aka ci amanar jam’iyyar APC, ake kuma ci gaba da cin amanarta.Kamar yadda masu sharhi suka fada lokuta daban-daban a kafafe daban-daban, babu wata dimokuradiyya da ke […]
Har yanzu talakawan Najeriya ba su gama fita daga daurewar kai game da abin da ya faru ko yake ma cikin faruwa a majalisar kasa ba, inda kiri-da-muzu aka ci amanar jam’iyyar APC, ake kuma ci gaba da cin amanarta.
Kamar yadda masu sharhi suka fada lokuta daban-daban a kafafe daban-daban, babu wata dimokuradiyya da ke aiki a majalisar kasa, illa son zuciya da munafunce-munafunce. Da munafunci ne Bukola Saraki ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, kazalika munafincin ne, ya kai Yakubu Dogara bisa wannan kujera.
Duk da kokarin da aka yi na ganin an sasanta wannan rikici to amma da alama, Saraki da Dogara ba za su taba sassauci ba kuma ba komai ya sa suke ci gaba da bijire wa uwar jam’iyya ba sai don saboda an ki daukar matakin hukunta su.
Ta yaya jam’iyya ko wata kungiya za ta tabbatar da biyayya da da’a a cikinta idan misali ba a iya hukunta wadanda kiri-da-muzu ke ci mata dundunniya ba?
Ga duk alamu, idan talakawan Najeriya suka ci gaba da zura na mujiya, to tabbas za a yi masu sakiyar da ba ruwa. Bara-gurbi wadanda suka shigo rigar Buhari za su dinga fakewa da guzuma don su harbi karsana. Misali, za su fake da ’yanci ko gashin kan majalisa wajen biyan bukatar siyasar kansu.
Akwai rawar da talakawa za mu iya takawa wajen taka wa ’yan-ina-da-mulki burki irin su shugabannin majalisun tarayya na yanzu. Za mu bi abin mataki-mataki. Yanzu tunda mun san abubuwan da Saraki da Dogara suke ba su dace da muradun hatta mutanen mazabarsu ba, to sai talakawan mazabar su fara rubuta masu wasika, inda za su bayyana rashin jin dadinsu game da yadda suke ci gaba da kawo wa jam’iyya tarnaki. Idan suka rubuta sai su aika masu, sannan su jira. Idan ba su fasa abin da suke ba, kuma ba su rubuto masu da martani ba, to sai su kara rubuta masa har sau uku. Idan duk wannan ba su yi, tasiri ba,sai su rubuta su buga a jarida ta kasa. Duk idan hakan ta gaza cin ma ruwa, to daga nan sai su fara tuntubar sauran talakawa tare da ilimantar da su a kan illar abin da wakilansu ke yi. Daga nan sai su fara shirye-shiryen yi masu kiranye, su maido su gida tun da ba bukatarsu suka je karewa ba.
To amma hakan ba zai yiwu ba sai an cire kwadayi, kabilanci, bangaranci, tsoro da bambancin addini. Lokaci ya yi da talakawan Najeriya za su nuna wa duniya cewa, sun fahimci dimokuradiyya da irin karfin da suke da shi a karkashin tsarin.
Wadannan bara-gurbin ’yan takara, tunaninsu shi ne, ba za a iya yi masu kiranye ba, don haka za su iya duk abin da suke so saboda suna ganin suna da shekaru hudu da za su murda abubuwa kafin zabe.
Bishir ya rubuto daga Sabuwar Unguwa Katsina (08165270879)