Taya murna ga Shugaba Buhari
Assalamu Alaikum, jaridar Aminiya mai farin jini ku ba ni dama na mika sakon taya murna ga sabon Shugaban kasar Najeriya wato Janar Muhammadu Buhari game da nasarar lashe zabe da ya yi a shekaranjiya Laraba. A gaskiya wannan abin farin ciki ne ga dimbin al’ummar kasar nan dama sauran sassan duniya baki daya. A […]
Assalamu Alaikum, jaridar Aminiya mai farin jini ku ba ni dama na mika sakon taya murna ga sabon Shugaban kasar Najeriya wato Janar Muhammadu Buhari game da nasarar lashe zabe da ya yi a shekaranjiya Laraba. A gaskiya wannan abin farin ciki ne ga dimbin al’ummar kasar nan dama sauran sassan duniya baki daya.
A hannu daya kuma ina kira ga Janar Buhari da ya yi amfani da wannan nauyi da Allah ya daura masa wajen kwatanta gaskiya da adalci a tsakanin al’ummar kasar nan. Na tabbata wannan shi ne kalubalen da yake gabansa. Har ila yau, ina sanar da duniya cewa ni ne nafi kowa murnar nasarar da Buhari ya samu a matsayinsa na zababben Shugaban kasa, saboda a karkashin gwamnatin jam’iyyar PDP ne aka kore mu daga makaranta, aka kona mana gidajenmu da ke garin Dambo’a, kana aka sanyamu gudun hijira.
Daga karshe muna addu’ar Ubangiji ya bai wa sabon shugaban ikon jagorancin al’ummar kasar nan baki daya, amin.
Daga Adamu Aliyu Ngulde, 08032135939
Allah Ka tallafa wa Janar Buhari
Salam Editan, Don Allah ku ba ni dama na nuna farin cikina bisa yadda Janar Muhammadu Buhari ya doke Shugaba Goodluck Jonathan. Ya Allah Ka tallafa wa Janar Buhari wajen yadda zai gudanar da mulkinsa cikin adalci ga al’ummar kasarmu. Daga karshe ina taya ‘yan Najeriya murna.
Daga Mudassir Ibrahim Mando, Kaduna, 08024122559
Gaskiya ta yi halinta
Zuwa ga Edita hakika lallai talakkawan Najeriya kun nunawa cewa kuna iya canza shugaba duk da magudin da akayi a wasu jahohin kuduncin kasar nan, bai hana malaman jami’a fadin sakamakon zabe na gaskiya ba kuma irin yadda mutane suka yi watsi da gwamnonin jahohin Neja Ma’azu Aliyu , Kebbi Saidu dakingari , Bauchi Isah Yaguda, Jigawa Sule Lamido , Binuwai Gabriel Suswan, domin wani zalunci da ake yiwa talakawan Arewa sune ke jagaba wajen zabensa da kuma kauda kai daga abubuwan da ke damun mutanen arewa. Yau dai gaskiya ta yi halinta mutane sun bukaci canji kuma sun sauya gwamnatin Najeriya daga jam’iyyar PDP zuwa APC Allah ka sa muga amfanin hakan.
Daga Usman Adamu Aliero, Jihar Kebbi, 07061594299
Taya murna ga ’yan Najeriya
Salam, Aminiya ku ba ni dama na taya ’yan uwana ’yan Najeriya masu neman canji a kasanmu murnan wannan nasara ta Janar Muhammadu Buhari. Ya zama zababben Shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC, a gaskiya wannan nasara ne ga duka talalawan kasar nan saboda amun mutum kamar Buhari, a irin wannan lokaci musamman idan aka duba irin halin da kasarmu ke ciki a yau ta matsalar tsaro da rashin aikinyi da tabarbarewan tattalin arzikin kasa. Allah ya taimaki sabon Shugaban, akan nufinsa na alheri ga Najeriya.
Allah Ya ba shi ikon rike talakawansa cikin gaskiya da adalci.
Daga Ahmadu Manager, Bauchi, 08065189242
Edita, Don Allah ka mika sakon murna ga mutanan kasar nan da ma na sauran kasashen duniya baki daya. Allah ya yi yau Janar Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasar nana. Allah taya shi riko. Ubangiji ya ba shi ikon sauke nauyin lafiya. Kuma ina kira ga Janar Buhari ya bar maganar kama mutanen da suka zaluncemu. Ya barsu da Allah shi zai saka mana anan duniya da lahira.
Daga Malam Usman Lawal Shehu Daura, 08062399922
Allah Ya taya Buhari riko
Alhamdulillah wassalatu wassalamu alarasulillah, Ya Allah ka taya zababben Shugaban kasarmu Muhammadu Buhari riko Ka kareshi Ka albarkaci gwamnatinsa da kasarmu ka ba mu lafiya da zaman lafiya amin.
Daga Mallam Abubakar Na’ibi
Darussan da za’a koya daga nasarar Janar Buhari
Tabbas akwai muhimman darussa da za mu amfana da su game da lashe zaben da Muhammadu Buhari ya yi a zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta wuce. Ga wasu daga ciki:
Na farko, mulki Allah ne yake ba da shi, idan ban da haka da bai ci zabe ba, saboda kwace mulki a hannun mai shi da kamar wuya. Na biyu, gaskiya da rikon amana suna da mutukar muhimmanci a rayuwa, Janar Buhari bai mallaki abin da zai iya tsayawa neman kujerar kansila ba, amma saboda gaskiyarsa mutane sun zabe shi kyauta a matsayin Shugaban kasa. Abu na uku shi ne, komai yana da ajalin da Allah ya sanya masa, ya tsaya takara har sau uku a baya ba tare da samun nasara ba, amma sai yanzu a karonsa na hudu.
Na hudu, zalunci ba ya dorewa, na dade ina ganin cewa Goodluck Jonathan ba zai ci wannan zaben ba, saboda azzalumi ba ya karko. Sai abu na biyar, wato muhimmancin komawa ga Allah, tabbas talakawa sun jima suna rokon Allah ya kawo musu canji, ga shi kuma Ya amsa addu’arsu.
Na shida, siyasar Najeriya ta fara canzawa, a kasa a tsare, a raka, a jira, a fada din, da talakawa suka yi yana nuna yadda mutane suka san ’yancinsu. Na bakwai kuma na karshe, duk shugaban da yake bin masalahar kansa bai damu da ta talakawa ba, to zai iya rasa kujerarsa a lokacin da bai zata ba.
Daga Usman Dan-Gunduman Jama’are, 081-63055770