Taya ni mu gyara (1)
Assalamu alaikum,a wannan satin za mu yi bayani ne a kan gudumawar da maza za su bayar wajen dora yara a kan hanyar da ta dace. Koda yake mata su ne suke tare da yara koda yaushe a gida. Amma hadin kai daga wurin maza yana da matukar muhimmanci, domin kuwa “Hannu daya ba ya […]
Assalamu alaikum,a wannan satin za mu yi bayani ne a kan gudumawar da maza za su bayar wajen dora yara a kan hanyar da ta dace. Koda yake mata su ne suke tare da yara koda yaushe a gida. Amma hadin kai daga wurin maza yana da matukar muhimmanci, domin kuwa “Hannu daya ba ya daukar jinka”.
Namiji shi ne shugaba a gida don haka shi Allah Ya dora wa alhakin jagorancin gida da sauran muhimman abubuwa da suka hada da ciyarwa da tufatarwa da sama wa iyali muhalli da ba su ilimi da kula da tarbiyya da sauran abubuwa da dama, ita mace mataimakiya ce.
Wani lokaci akan samu akasi ta yadda wasu mazan sukan yi sakaci wajen daukar nauyin wadannan hakkoki da Allah Ya dora musu. Wannan kuwa yakan kawo kalubale ga iyali baki daya, musamman yara, domin kuwa tarbiyyarsu tana shiga wani hali. Yawanci kalubalen da mata sukan fuskanta yayin tarbiyyar yara ya danganta ne da yanayin da suka tsinci kansu a ciki. Misali idan miji bai cika zama a gida ba, ko dai ba ya tare da iyalinsa saboda yanayin aikinsa, ko kuma aure ya mutu, ’ya’yan suna hannun mahaifiyarsu, ko yara su tsinci kansu a hannun matar da ya aura wadda akan kira matar uba, ko kuma iyaye suna tare amma ba ya son matarsa ta takura wa ’ya’yansa. Akan samu kuma iyayen da duk su biyun ba sa son laifin ’ya’yansu.
Akwai mazan da ba su cika zama a gida ba, kafin yara su tashi daga barci sun fita, lokacin da za su dawo kuma yara sun yi barci. Wasu kuwa kwata-kwata ba sa gari, kuma sukan dade ba su leko gidajensu ba balle su san abin da iyalinsu suke ciki. Za ka tarar namiji bai san irin fadi- tashin da mace take yi ba wajen kula da harkokin gida da yara. Irin wannan yanayi yakan jefa iyali a cikin halin kaka-nika- yi. Domin kuwa babu ci, ba sha, ba suturar kirki, ba lafiya, ba kudin sayen magani, ba natsuwa da sauran matsalolin da ya jefa su a ciki.
Idan kuwa aka yi rashin sa a aure ya mutu, iyali, musamman yara sukan shiga wani hali mawuyaci. Domin kuwa sukan tsinci kansu kodai a hannun mahaifyarsu ta yadda za ka ga abinci ma yana yi musu wahala balle kula da iliminsu. Wanda shi ne jigon tarbiyya, saboda mahaifiyarsu ba za ta iya daukar nauyinsu ba. Mahaifinsu kuma tun da aure ya mutu ba zai kara waiwayarsu ba balle ya sauke nauyin da Allah Ya dora masa.Wani namijin ma cewa yake ya bar mata ’ya’yan, tun da ya sallama mata ’ya’ya kuwa ba zancen ya tuna da su balle ya tuna da hakkinsu a kansa. Koda yake wasu mazan sukan kwashe ’ya’yansu su kai wa matarsu da niyyar su ci gaba da kula da su, amma ba a cika samun nasara ba a irin wannan yanayi. Yawanci matan uba ba su cika kula da ’ya’yan da ba su suka haifa ba.
Za mu ci gaba in sha Allah!