Taye Taiwo ya koma Finland

Shahararren dan kwallon Najeriya Taye Taiwo ya koma Finland inda yanzu haka yake buga wa kulob din HJK Helsinki kwallo.  Tuni ma dan kwallon ya fara bugawa kulob din wasa a ranar Litinin da ta gabata bayan sun tashi kunnen doki (1-1) da kulob din HIFK a gasar rukunin kasar.Tsohon dan kwallon kulob din Olympikue […]

Taye Taiwo ya koma Finland
Taye Taiwo ya koma Finland

Shahararren dan kwallon Najeriya Taye Taiwo ya koma Finland inda yanzu haka yake buga wa kulob din HJK Helsinki kwallo.  Tuni ma dan kwallon ya fara bugawa kulob din wasa a ranar Litinin da ta gabata bayan sun tashi kunnen doki (1-1) da kulob din HIFK a gasar rukunin kasar.
Tsohon dan kwallon kulob din Olympikue Marseille da ke Faransa ya koma Finland ne bayan ya shafe watanni 16 ba tare da ya yi kwallo ba saboda rauni.
Daraktan kula da sha’anin wasanni na kulob din HJK Helsinki ya bayyana matukar farin cikin ganin sun samu Taye a matsayin dan kwallon da zai yi musu wasa a kakar wasa ta bana.  “Mun yi matukar farin ciki da Taye Taiwo ya amince zai yi wa kulob dinmu kwallo.  Yana da kwarewa sosai musamman idan aka yi la’akari da yadda ya yi wa manyan kungiyoyin kwallon kafa a sassan Turai kwallo”, inji shi a wata sanarwa da ya fitar a kafar sadarwar kulob din.
Sai dai bayanai sun nuna Taye Taiwo ya koma kulob din ne a matsayin aro kafin karshen kakar wasa ta bana amma akwai yiwuwar kulob din ya saye shi a matsayin dan kwallonsu na dindindin idan ya yi kokari.