Taye Taiwo ya koma Turkiyya

Shahararren dan kwallon Super Eagles Taye Taiwo ya canza sheka daga kulob din AC Milan da ke Italiya zuwa na Bursaspor da ke Turkiyya.A kakar wasan da ta wuce ne dai kulob din Milan ya tura Taye Taiwo Ukraine a matsayin aro, inda ya bugawa  kulob din Dynamo Kieb.Taye ya sanya wa kulob din Buraspor […]

Taye Taiwo ya koma Turkiyya
Taye Taiwo ya koma Turkiyya

Shahararren dan kwallon Super Eagles Taye Taiwo ya canza sheka daga kulob din AC Milan da ke Italiya zuwa na Bursaspor da ke Turkiyya.
A kakar wasan da ta wuce ne dai kulob din Milan ya tura Taye Taiwo Ukraine a matsayin aro, inda ya bugawa  kulob din Dynamo Kieb.
Taye ya sanya wa kulob din Buraspor hannu ne a kwantaragin shekara uku bayan ya yi nasarar gwaje-gwajen da likitoci suka yi masa don tabbatar da lafiyarsa.
dan shekara 28, Taye ya koma AC Milan ne daga kulob din Marseille da ke Faransa a shekarar 2011 amma ya kasa tabuka abin a zo a gani da hakan ta sa ya koma benchi.
Hakan ta sa kulob din Milan ya aika da shi zuwa kulob din kueens Park Rangers (kPR) da ke Ingila bayan ya kammala ne sai kuma aka sake tura shi Ukraine yanzu da ya kammala ne kwantaraginsa ta kare da Milan kuma ya tattara nasa-ya-nasa ya bar kulob din.
Bayan ya kammala kwantaraginsa da kulob din Milan ne ya yanke shawarar raba-gari da kulob din inda yanzu haka ya koma Turkiyya don cigaba da buga kwallo.
A game da zancen sake kiransa don buga wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kuwa, Taye ya ce wannan shawara tana wurin koci Stephen Keshi ne amma zai yi duk mai yiwuwa ya kayatar don ganin an sake kiransa don buga wa kasar haihuwarsa.