Tazarar Haihuwa: Abubuwan Kiyayewa

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan ka’idojin da ya kamata ma’aurata su duba kafin aiwatar da tazarar haihuwa. Da fatan Allah Ya sa bayanin ya isa ga masu bukatarsa, musamman […]

Tazarar Haihuwa: Abubuwan Kiyayewa
Tazarar Haihuwa: Abubuwan Kiyayewa

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan ka’idojin da ya kamata ma’aurata su duba kafin aiwatar da tazarar haihuwa. Da fatan Allah Ya sa bayanin ya isa ga masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da tambayoyi, amin.
ka’idojin Kiyayewa:

Akwai abubuwan kiyayewa da ya kamata ma’aurata masu niyyar aiwatar da tazarar haihuwa tsakanin ’ya’yansu su yi la’akari da su kafin su fara:
1.    Cancanta: Yana da kyawu ma’auratan da suka kuduri niyyar fara yin tazarar haihuwa su zauna su yi kyakykyawan nazari, kuma su auna su gani, shin sun cancanta da su ba da tazarar haihuwa? Misali, ma’auratan da ba su da wata matsala ta lafiya, kuma suna da karfin hikimar baiwa ’ya’yansu kyakkyawar tarbiyya, kuma suna da halin da za su biya a taya su kula da ’ya‘ya, ga kuma dukiyar iya ciyar da ’ya’yan, shin wadannan sun cancanta su ba da tazarar haihuwa? Shin yanzu suna da hujjar da za su dogara da ita a addinance, wacce ta wajabta musu yin tazarar haihuwa? Tabbas irin wadannan ma’aurata ba su da wata hujja musamman idan aka yi la’akari da cewa yin tazarar haihuwa makaruhi, watau an so kada Musulmi ya yi shi ba tare da wata babbar lalura ba, amma idan ya yi din to ya halatta. Kamar yadda wani dan uwa ya aiko da bayani a kan irin haka da ke yawan faruwa cikin al’umma:
“Malama ni abin da na lura da shi a kasarmu ta Hausa shi ne: Masu kudi da ’yan boko da masu ilmi su ne suka fi yin amfani da hanyoyin kayyade iyali ko na tazarar haihuwa; ni kuwa a gani na su ya fi dacewa a ce sun tara iyali, don mai kudi yana da halin kula da bukatun ’ya’yansa ba tare da ya yi tazarar haihuwa ba, mai ilmi zai ba ’ya’yansa ilmi, kuma ya ba su tarbiyya sannan ya kasance ba su tagayyara ba a rayuwa. Bisa la’akari da Hadisin Annabi SAW da Ya ce ku yi aure ku hayayyafa, don in yi alfahari da yawanku ranar lahira.’ Shin ko ya halatta mai kudi ya yi tazarar haihuwa ko ya kayyade iyalinsa?
—Malam Muttaka Zaria.
Amsar wannan tambaya ta Malam Musa ita ce: kwarai kuwa ya halatta ga mawadacin mai arziki ya ba da tazarar haihuwa kamar yadda ya wajaba ga talaka, domin a Musulunce babu bambancin hukunci tsakanin talaka da mai kudi, don haka ya halatta mai kudi ya ba da tazarar haihuwa matukar ya cika sharuddan yinsa. Abin takaici ne a ce masu kudi kuma masu ilmi suke kyamar haihuwa, amma talaka shi kuma yake kyamar rashin haihuwa. Wannan ne ya sa talakawa da marasa ilmi suka fi yawa a cikin al’umma.
2.    Kyautata Niyya: Shi ne gabatar da ayyuka don Allah kadai ba tare da biye wa son zuciya ba. Yana da matukar muhimmanci ma’aurata su rika tunawa da Allah Madaukakin Sarki yayin da suka kudiri aniyar yin tazarar haihuwa. Domin yana da matukar alfanu ga rayuwar duniya da lahirar mutum ya kasance duk lokacin da zai yi wani zabi, ya zabi abin da ya fi kyawu a wajen Allah SWT, ya kuma kauce wa bin son zuciyarsa da son more rayuwar duniya. Da yawan wasu matan sukan dakatar da haihuwa wai don su huta da dawainiyar daukar ciki, haihuwa da renon yara, alhali lafiyarsu da ta yaran da suke haihuwa ba ta samu matsala ba a dalilin haihuwar da suke yi. Sun manta da dimbin ladar da suke samu a dalilin haka; ba su san cewa Allah Madaukakin Sarki na iya kade masu wata masifa ko wata fitina ba a dalilin dawainiyarsu? Haka kuma akwai mazan da ba su son matansu su haihu don dorewar samun biyan bukatar sha’awarsu kadai, domin haihuwa na samar da canji ga ‘yan matancin mata, wanda wannan na rage dandanon ibadar aure. Don haka yin komai don Allah ya fi kawo albarka sama da biye wa soye-soyen zuciya da ba su da tabbas.
3.    Amincewar Juna: Dole sai dukkan ma’aurata sun amince da yin tazarar haihuwa kafin a aiwatar da shi; in miji naso mata ba ta so, dole mijin ya hakura, haka kuma in matar ce ke so mijin ba ya so ita ma dole ta hakura. Domin samun haihuwa muhimmin abu ne da ya sa ake kulla aure dominsa, don haka bai halatta ba daya ya danne wa daya hakkinsa na samun zuri’a. Kamar yadda aka samo daga Annabi SAW cewa “bai halatta Maigida ya yi azalu da matarsa ba sai da amincewarta,” don yin azalun na rage mata jin dadin ibadar aure da kuma hana haihuwa. Don haka haramun ne maigida ya tilasta matarsa yin tazarar haihuwa alhali ba ta so. Haka ita ma matar bai halatta a gare ta ta yi wani abin da zai hana ta daukar ciki ba tare da sani ko amincewar mijinta ba.

4.    Zabar Hanya Mafi Dacewa: Lokacin zaben samfurin hana shigar cikin da ma’aurata za su yi amfanai da shi, sai su zabi wanda yake ba zai zama mai cutarwa ga uwa ko  dan da take goyo ba. Don haka dole sai ma’aurata sun yi bincike mai kyawu da nazarin duka hanyoyin dakatar da haihuwa, don zabar mafi dacewa ga uwargida a lokacin. Wanda ake ganin ya fi kyawu ko ya fi yin suna wajen hana haihuwa ba lallai ne ya zama ya dace da kowace mace ba, domin kowane dan Adam yanayin jikinsa daban da na wani, abin da ya yi wa wannan, ya dace da yanayin jikinsa ba lallai ya yi haka ga waninsa ba.
Sai sati na gaba In sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.