Teba ta kwantar da matashi tsawon shekara 10

Wani matashi dan shekara 28 a kasar Saudiyya, Adam Mohammad AbdulHamid Al-Jasim, nauyin jikinsa na kilo 400 da matsananciyar teba sun kwantar da shi har tsawon shekara 10. Wannan nauyin jiki ya hana shi motsi ko tafiya, ballanta ma ya yi rarrafe. Wannan matashi yabna fama da cutar matsananciyar teba, al’amarin da ya kwantar da […]

Teba ta kwantar da matashi tsawon shekara 10
Teba ta kwantar da matashi tsawon shekara 10

Wani matashi dan shekara 28 a kasar Saudiyya, Adam Mohammad AbdulHamid Al-Jasim, nauyin jikinsa na kilo 400 da matsananciyar teba sun kwantar da shi har tsawon shekara 10. Wannan nauyin jiki ya hana shi motsi ko tafiya, ballanta ma ya yi rarrafe.

Wannan matashi yabna fama da cutar matsananciyar teba, al’amarin da ya kwantar da shi har tsawon shekara 10. Yana zaune ne a wani gida mai fadin mita 40 da ke Al-Hofouf a yankin Al-ahsa da ke kasar Saudiyya.
Ya ce: “Na daina zuwa makaranta bayan da na kamala karatun Firamare, saboda zaman gida sai kiba da nauyi suka far mini cikin kankanen lokaci, kuma tunda wancan lokacin na kasa yin wani motsi.”
Duk da matsanancin halin da yake ciki, Al-Jasim ba shi da rajista a wata cibiya ta kula da walwala da kyautata jin dadin al’umma, alhali yana fama da talauci;kuma gidan iyayensa cike yake da kwari da beraye.
Al-Jasim ya ce burinsa ya samu faragar yin tafiya, ta yadda zai samu aikin yi, don kyautata halin rayuwar da yake ciki. Ya kuma daina zuwa babban Asibitin Sarki AbdulAziz na sojan kasa da ke Al-Ahsa, saboda matsalar da ake samu wajen kai shi asibitin.
Al-Jasim ya mika godiyarsa ga wani dan kasuwa Basim Alghadeer, saboda irin tallafin da yake ba shi, amma ya yi nuni da cewa matsananin halin da yake ciki na bukatar kula da talalfi na musamman, kamar yadda jaridar Arabnews ta ruwaito.