Tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (7)
Shahararrun Bulaguro (II)A shekarar 1858 sai lamarin ya canza salo. Daga bulaguron bude ido ko ganin ikon Allah, zuwa samar da hanyoyin sadarwa. Cikin wannan shekara ne Cyrus West Field ya shimfida wayar kebul, don aiwatar da sadarwa ta amfani da na’urar Telegraph. Shi ne mutum na farko da ya fara shimfida wannan waya a […]
Shahararrun Bulaguro (II)
A shekarar 1858 sai lamarin ya canza salo. Daga bulaguron bude ido ko ganin ikon Allah, zuwa samar da hanyoyin sadarwa. Cikin wannan shekara ne Cyrus West Field ya shimfida wayar kebul, don aiwatar da sadarwa ta amfani da na’urar Telegraph. Shi ne mutum na farko da ya fara shimfida wannan waya a karkashin Tekun Atlantika da wannan manufa. Wannan yunkuri na cikin abubuwan da suka taimaka wajen habbaka tsari da hanyoyin sadarwa na zamani a zamunnan baya, kafin wannan lokaci.
Daga cikin bulaguron da suka ajiye tarihi a Tekun Atlantika har wa yau, akwai yunkurin da wani babban jirgin ruwa mai suna: “RMS Titanic” ya yi, inda ya taso daga kasar Birtaniya a birnin Ingila ya nufi kasar Amurka, amma kafin tafiya ta yi nisa, ya ci karo da wani tsaunin kankara, wanda sanadiyyar haka ne ya huje, ruwa ya cika jirgin daga kasa ba tare da sanin matukansa ba, har a karshe dai ya sulmuya tare da hallakar da mutane sama da 1,500. Wannan lamari ya faru ne a ranar 15 ga watan Afirilu, shekarar 1912. Na san masu karatu sun san kadan daga cikin tarihin wannan lamari, musamman ganin cewa akwai fim na musamman da aka shirya mai suna: “Titanic” a shekarar 1997, daidai lokacin da lamarin ya cika shekara 85 da aukuwa ke nan.
Da yawa cikin matasa na ganin jigon wannan fim ne a bangaren soyayya kadai. Sai dai babban jigon shirin shi ne kokarin tabbatar da girma da abin al’ajabin da ya faru a kan wannan jirgi. Domin jirgi ne da kafin a kera shi, ba a taba samun jirgin ruwa mai girma irinsa ba. Amma sai ga shi ya ci karo da tsaunin kankara dake karkashin teku, har ya sulmuya.
Abu na biyu shi ne, lamarin gaba dayansa ya auku ne a Tekun Atlantika, a wani yunkuri na ketare tekun ta amfani da wannan babban jirgin ruwa. Wanda da a ce hakan ya yiwu, da ya zama babban abin tarihi fiye da na baya, kan abin da ya shafi ketare Tekun Atlantika. Amma sai dai kash, ba haka Allah ya tsara kuma yaso ba.
Cikin watan Mayu na shekarar 1915, ranar 7 ga wata ke nan, wani katon jirgin ruwa mai suna: “RMS Lusitania” shi ma, ya yi yunkurin ketare Tekun Atlantika a hanyarsa ta zuwa kasar Ireland. Amma ya hadu da hadarin yaki, inda wani makamin mizayil na karkashin teku ya harbe shi kai tsaye; inda mutum dubu da198 ne suka rasa rayukansu. Wannan bulaguro bai kai ga gaci ba. Amma lamarin gaba daya ya auku ne a kan Tekun Atlantika.
Daga cikin yunkurin kerare Tekun Atlantika da tarihi ya taskance mana akwai wani shahararren atisayen jiragen ruwan yaki don shirya wa yakin duniya na daya. Wannan atisaye ya faru ne tsakanin shekarun 1914 zuwa 1918. Wannan atisaye da aka gudanar a Tekun Atlantika ya haifar da hadari mai girman gaske, inda jiragen ruwan yaki guda 2,100 suka nutse, sannan kananan kwale-kwalen yaki guda 53 suka hallaka.
A shekarar 1919 kuma sai ga wani yunkuri na tsallaka Tekun Atlantika daga kasar Amurka. An gudanar da wannan bulaguro ne da wani nau’in jirgin saman ruwa, wato: Seaplane na kasar Amurka mai suna: NC-4. Da wannan jirgi aka yi nasarar tsallaka Tekun. Kuma shi ne nau’in jirgin ruwan sama na farko a duniya da ya tsallaka Tekun Atlantika a tarihin tekun. Wadanda suka tsallaka tekun da wannan jirgi sun yi haka ne a shekarar 1919, kamar yadda ya gabata. A shekarar 1927 kuma sai wani shahararren matukin jirgin sama mai suna: Charles Lindbergh, shi kadai, ba tare da wani abokin rakiya ba, ya tsallaka Tekun Atlantika daga farko har zuwa karshensa, ba tare da ya yi Zango a wani wuri ba. Charles ya taso ne tun daga birnin Paris na kasar Faransa, ya dire a birnin New York na kasar Amurka, bayan tsallako tekun gaba dayansa. Shi ne na farko a duniya da ya fara tsallaka tekun ba tare da abokin rakiya ba kuma ba tare da yin Zango a ko ina ba.
A shekarar 1932 sai bulaguro cikin Tekun Atlantika ya canza salo, daga mazaje masu jaruntar tuki ko sarrafa jiragen ruwa, zuwa mata masu kama da maza. Mace ta farko da ta fara tsallaka Tekun Atlantika ita kadai ba tare da aboki ko abokiyar rakiya ba ita ce: Amelia Earhart. Wannan mace mai kamar maza ta taso ne tun daga tsibirin kasar Kanada mai suna: Newfoundland, inda ta tike da Arewacin kasar Ireland da ke nahiyar Turai.
Daga cikin bulaguro da aka yi amma da manufar yaki, akwai wanda ya auku tsakanin shekararun 1939 – 1945, wanda ya zama wani bangare na Yakin Duniya na biyu. Wannan yaki da aka yi shi a cikin Tekun Atlantika tsakanin wadannan shekaru, ya haifar da nutsewar jiragen ruwan yaki guda 3,700. Tirkashi!
A shekarar 1952 kuma sai ga wata macen mai suna: Ann Dabidson wacce ita ma, kamar ’yar uwarta Amelia, ta tsallaka tekun ita kadai a jirgin ruwa. Ann Dabidson ta zama ta biyu wajen jarumta a wannan fanni ko bangare, a tarihin masu bulaguro cikin Tekun Atlantika.
Ana shiga shekarar 1984, sai ga wani jarumi mai suna Amyr Klink, wanda ya tsallaka Tekun Atlantika cikin kwanaki 100, ta amfani da kwale-kwale, shi ma shi kadai. Klink ya faro bulaguronsa ne daga bakin gabar Tekun Atlantika da ke kasar Namibiya, ya tuke a bakin gabar da ke kasar Burazil. A kwale-kwale. Shi kadai. Cikin kwanaki 100. Lallai ya sha sanyi.
Bayan shekaru 10 (a shekarar 1994), sai ga Guy Delage, shahararren dan ninkaya a cikin teku, ya tsallaka Tekun Atlantika da ninkaya. Babban magana! Guy Delage dai shi kadai ne yayi wannan kuru, ta amfani da jirgin ruwan fito, inda ya taso daga tsibirin Cape berde zuwa tsibirin Barbados da ke nahiyar Karibiyan (da jirgin ruwan fito). Daga nan ya ajiye jirgin ruwan fiton, ya fara ninkaya daga tsibirin/garin Benoit Lecomte, har ya tsallaka Tekun Atlantika da ninkaya. Sau daya kawai yayi Zango na kwanaki 10 a tsibirin Azores. Wannan bawan Allah ya ciri tura cikin masu bulaguro a Tekun Atlantika, sanadiyyar amfani da ninkaya wajen tsallakawa. Wata jarumtar sai da sayar da rai.
A shekarar 1999 kuma sai ga wata macen kuma mai suna: Tori Murden, wacce ta tsallaka Tekun Atlantika ta amfani da jirgin kwale-kwale, cikin kwanaki 81. Masu kididdiga suka ce ta ci tazarar kilomita 4,767 ne a wannan bulaguro nata, daidai da tazarar mil 2,962 kenan. Malama Tori ta fara bulaguronta ne daga bakin gabar tekun da ke Gualdeloupe, inda ta tuke a tsibirin Canary (Canary Islands) Turkashi!
Da zamani ta kara gaba, aka samu karin hikimomi cikin fasahar kere-kere, sai ga wani jarumi mai suna: Alan Priddy, tare da ‘yan rakiyarsa guda uku, ya tsallaka Tekun Atlantika ta bangaren Arewaci (North Atlantic Ocean), cikin sa’o’i 103, wato cikin kwanaki 4 ke nan! Ba wannan ba ne kadai abin mamaki, Alan ya yi wannan tafiya ne ko bulaguro ta amfani da jirgin ruwan roba irin ta zamani mai suna: Rigid-hulled Inflatable Boat (RIB), inda ya taso daga tsibirin kasar Kanada dake bakin gabar tekun mai suna: Newfoundland, ya ratsa ta tsibirin Greenland, inda a karshe ya tike a kasar Scotland. Duk wannan cikin kwanaki hudu. Wannan, a binciken malaman tarihi, na nuna shi ne wanda ya tsallaka Tekun Atlantika cikin mafi karancin lokaci, ta amfani da abin hawa mafi hadari. Wannan lamari ya faru ne a shekarar 2003.
Wadannan, a babin takaitawa, su ne kadan daga cikin suka kutsa Tekun Atlantika da nufin bulaguro ko wata bukata ta musamman, a tarihin tekun a duniya.