Tela ya jawo wa kansa jangwam
Wani matashi mai suna Malam Bala Abdurrahman Tungo, dan asalin kauyen Tungo a karamar |Hukumar Sule-Tankarkar ta Jihar Jigawa da ke zuwa Kalaba cirani yana sana’ar dinki ya jawo wa kansa shiga halin kaka-nika-yi sakamakon askar gashin wani yaro da almakashi ya sanya aljihunsa, kamar yadda mahaifiyar yaron ta shaida wa ’yan sanda. Ranar Talatar makon […]
Wani matashi mai suna Malam Bala Abdurrahman Tungo, dan asalin kauyen Tungo a karamar |Hukumar Sule-Tankarkar ta Jihar Jigawa da ke zuwa Kalaba cirani yana sana’ar dinki ya jawo wa kansa shiga halin kaka-nika-yi sakamakon askar gashin wani yaro da almakashi ya sanya aljihunsa, kamar yadda mahaifiyar yaron ta shaida wa ’yan sanda.
Ranar Talatar makon jiya ne a wani layin Palm da ke yankin karamar Hukumar Kalaba ta Kudu aka kira shi domin ya yi wa wata mata dinkin tsummokaranta. Yayin da uwar yaron ta ajiye danta kusa da telan, kafin ta shiga daki ta tattaro masa kayan da zai dinke, sai ya fakaici idonta, ya sanya almakashi ya aski wani sashe na gashin kan yaron. Ko da matar ta fito ta ga kan danta ba kamar yadda ta bar shi tare da tela ba, sai ta tambayi me ke faruwa, sai ya ce ai wasa yake yi da yaron. Hankalinta dai bai kwanta ba, saboda ba ta san dalilin yankar gashin danta ba, lamarin da ya jaza ta sanar wa rundunar ’yan sanda da ke gundumar Atakpa, domin daukar mataki. Yayin da ’yan sanda suka je gidan, shaidun gani da ido sun tabbatar cewa ya kunshe gashin ne a wata leda, ko da ’yan sandan suka bincika, sun same shi da kullin kambu da wasu layu.
Daga bisani, wanda ake zargi ya yi wa Aminiya karin bayanin, cewa yana wasa da yaron ne, “Sai tsautsayi ya dauke ni na yi masa aski da almakashi. Tsautsayi ne Allah Ya dora mini babu yadda zan yi.” Inji shi.
Ita kuwa mahaifiyar yaron mai suna Mary Ogon, ta shaida wa wakilinmu cewa, “dana shekararsa biyu, telan jeka-ka-dawo ne da muke kira ‘aboki’, ya shigo layinmu zai yi wa wasu dinki, sai mu ma muka ce idan ya gama, ya zo zai yi mana. Daga bari in shiga daki in dauko masa kayan, sai na ga an aski gashin yaro da ke kusa da shi yana yi masa wasa. Ashe da wata manufa. Dalilin da ya bayar shi ne ya tsaya kai da fata shi wasa yake da yaron, mu kuma hakan ba hujja ba ce gare mu.” Inji ta.
A lokacin rubuta rahoton dai ana tsare da shi a caji-ofis na Atakpa ana yi masa bincike da zarar an gama za a gurfanar da shi gaban kotu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Kuros Riba, Mista Hogan Bassey ya tabbatar wa wakilinmu afkuwar lamarin.