Teloli kaɗan ne suka samu ɗinkin Sallah a Kalaba
Gaskiya abin sai a hankali, domin babu kudi a hannun mutane, ga kaya sun yi tsada.
Wasu mazauna Jihar Kuros Riba sun nuna damuwa kan yadda Sallar bana ta zo musu a wani yanayi na kuncin rayuwa da rashin kudi da tsadar abinci.
Da dama iyayen yara sun kasa yi wa ’ya’yansu dinkin Sallah balle a yi maganar yi wa mata atamfar tashin Asuba kamar yadda aka saba a baya.
- Kamfanonin jiragen sama sun koka kan karancin fasinjoji
- Sallah ta yi armashi a Benin duk da rashin kudi
Bincike da Aminiya ta yi a Kalaba ya gano shagunan teloli a bana ba su samu yawan mutanen da suka saba kawo musu dinki ba saboda kuncin rayuwa da karancin kudi a hannun jama’a.
Salisu Tasi’u wani tela ne da ke zaune a Nasarawa Bacoco a Karamar Hukumar Birnin Kalaba ya shaida wa wakilinmu cewa a harkar samu a sana’ar ba kamar a baya ba, kasancewar mutane da yawa na kukan rashin kudi.
“Mutanen da ke kawo min dinkin Sallah na iyalansu kamar iri biyu a bana da kyar suka iya kawo daya saboda tsadar rayuwa da karancin kudi a hannun jama’a. Yanzu kowa ta kai yake yi,” inji shi.
Asiya Kabiru mai sayar da atamfofi a Unguwar Esuk Utang da ke garin Kalaba da wakilinmu ya zanta da ita ta ce, tunda take sayar da atamfofi da kayan yara ba ta taba ganin irin na bana ba.
“Gaskiya abin sai a hankali, domin babu kudi a hannun mutane, ga kaya sun yi tsada dama kuma muna aikawa garin Aba a Jihar Abiya da kuma Kasuwar Kwari a Kano muna saro kaya. To yanzu ko’ina ka taba sai tsada.
“Ga wadanda za su dauko maka ga kuma su kansu kayayyakin farashi kan sari ya kara kudi, wasu kuma ya ninka. Idan muka tambayi dillalan sai su ce da mu ba laifin su ba ne.
“Ko su ce farashin Dala ya tashi ko sun sha wahala wajen shigo da kayan. Ga kuma karin kudin sufuri da wahalhalun hanya kafin kayan su zo, shi ya sa komai ya canja.
“Kazalika wasu ma zuwa suke yi su taya kudin yadin sai su juya da niyyar za su dawo su saya, amma sai ka ji shiru. Haka muke wuni cinikin sai a hankali,” in ji ta.
Ta ce tunda aka zo jajibarin Sallah ba a ga ana hada-hadar sayen yadi ba, to, lallai shekarar ta zo wa mutane a murde.
Ustaz Yusuf Zakariya, malamin da Kungiyar Izala ta turo Kalaba don yin tafsiri, a lokacin rufe tafsirin bana ya yi kira ga al’ummar Musulmi su koma ga Allah, kowa ya yawaita tuba ga Allah tare daidaitawa da kuma kyautata tsakanin kowa da Mahalicci.