TETFund ta fara amfani da dalibai wajen duba gine-ginenta a manyan makarantu
Hukumar ta hakan zai sa ’yan kwangila su yi abin da ya dace
Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu na Najeriya (TETFund) ya fara amfani da Kungiyar Dalibai ta Najeriya (NANS) wajen duba gine-ginen da yake yi a makarantunsu.
Shugaban asusun, Sunny Echono ne ya bayyana hakan lokacin da yake bayar da kyautar wata motar bas mai cin mutum 30 ga NANS a Abuja ranar Litinin.
Ya ce daukar matakin ya zama wajibi saboda a rika sanya idanu yadda ya kamata a kan ’yan kwangilar da ke yin ayyukan.
Sonny ya kuma ce idan suna amfani da daliban, hakan zai sa su kasance suna da idanu da kunnuwa a makarantun, musamman kasancewar su daliban ne za su amfana da ayyukan.
Shugaban na TETFund ya kuma ce sun ba kungiyar gudunmawar motar ce domin saukaka musu zirga-zirga a tsakanin makarantu.
Da yake mayar da jawabi, shugaban NANS, Usman Barambu, ya yaba wa asusun saboda kyautar motar, bayan rokon da suka yi ga Shugaban Kasa Bola Tinubu a kwanakin baya.