Theresa May ta zama Firaministar Biritaniya
A shekaranjiya Laraba ne Firaministan Biritaniya, Dabid Cameron ya mika ragamar mulkin kasar ga sabuwar Shugabar jam’iyyar Conserbatibe Theresa May.Mista Cameron ya bar mukamin ne bayan shafe shekara shida, sai dai zai ci gaba da wakiltar mazabarsa a majalisar dokokin Biritaniya.Tuni dai ya kwashe kayansa daga fadarsa da ke Downing street.Theresa May ‘yar shekara 59 […]
A shekaranjiya Laraba ne Firaministan Biritaniya, Dabid Cameron ya mika ragamar mulkin kasar ga sabuwar Shugabar jam’iyyar Conserbatibe Theresa May.
Mista Cameron ya bar mukamin ne bayan shafe shekara shida, sai dai zai ci gaba da wakiltar mazabarsa a majalisar dokokin Biritaniya.
Tuni dai ya kwashe kayansa daga fadarsa da ke Downing street.
Theresa May ‘yar shekara 59 yanzu za ta zama mace ta biyu da ta rike matsayin Firaministar Biritaniya.
Za ta karbi ragamar a daidai lokacin da kasar ke fuskantar manyan kalubale tun bayan kuri’ar raba gardama da ta amince kasar ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai.
A da Mista Cameron ya bayyana cewa zai sauka daga mulki ne a watan Oktoba mai zuwa, amma saboda halin rashin tabbatar da kasuwannin hada-hadar kudi na duniya suka shiga saboda aniyyar kasar na ficewa da EU, hakan ya sa shi gaggauta sauka daga mulki gabanin lokacin da ya so tun farko.
Abin da ya sa masana suke ganin cewa matakin nasa zai taimaka wajen daidaita al’amura a nahiyar Turai da kuma duniya baki daya.