Threads: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan sabuwar kishiyar Twitter

Sama da mutum miliyan 10 ne suka bude shafi a dandalin cikin kwana 1

Threads: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan sabuwar kishiyar Twitter

Dandalin Threads

Sama da mutum miliyan 10 ne suka bude shafinsu a sabon dandalin Threads, wanda Meta, mamallaka shafin sada zumunta na Facebook suka kirkira don ya zama kishiyar Twitter.

Mamallakin kamfanin na Meta, Mark Zuckerberg ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis.

Sabon dandalin dai ya fara aiki ne a kasashe fiye da 100 da misalin karfe 12:00 na safiyar Laraba a agogon Najeriya da Nijar, kuma yanzu haka ana iya sauke shi a kan wayoyin Apple da Android.

Sai dai an samu tsaikon sakin shi a kasahen Turai, saboda batutuwan da ke da jibi da kare hakkin masu amfani da intanet.

Ana sa ran dandalin zai kasance babbar kishiya ga Twitter, wanda a dan tsakanin nan shafuka da dama ke barazanar kwace mata mabiya, kodayake ba su kai ga yin hakan ba.

Ga wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani a kan wannan sabon dandali:

  • Masu amfani da shafin za su iya rubutu da haruffa har guda 500, kuma yana da abubuwa da dama masu kamanceceniya da shafin Twitter.
  • Ko da mutum ya goge shafinsa a kan dandalin, hakan ba zai shafi shafinsa na Instagram ba.
  • Duk dan shekara 12 zuwa sama zai iya bude shafi a cikinsa, kuma za a same shi a harsuna fiye da 31, ciki har da Ingilishi da harsunan kasashen China da Rasha da Spaniya.
  • Babu wahalar bude shafi a dandalin; za ka iya budewa da bayanan shafinka na Instagram. Zai taho da dukkan bayananka da suke can, sannan za ka iya yin gyara domin su dace da shi.
  • Dandalin zai dauki tsaron masu amfani da shi da muhimmanci, sannan zai tabbatar ana bin dokokin amfani da shafi, irin na Instagram, sau da kafa.

Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM

Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi

’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina

Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike