Tianshin ’Yan mata: Shayi ko aji-garau

Editan Aminiya ka bani dama in yi tsokaci kan ’yan matan da ke yawo da tukunyar shayin tianshi a Abuja, suna sayarwa a kan kudi Naira 50. Lallai kamata ya yi mutane su yi hattara da shaye-shaye, domin ba a hakakke kan cewa ko tianshin ne suke sayarwa ba. Neman kudi na iya sanyawa a […]

Tianshin ’Yan mata: Shayi ko aji-garau
Tianshin ’Yan mata: Shayi ko aji-garau

Editan Aminiya ka bani dama in yi tsokaci kan ’yan matan da ke yawo da tukunyar shayin tianshi a Abuja, suna sayarwa a kan kudi Naira 50. Lallai kamata ya yi mutane su yi hattara da shaye-shaye, domin ba a hakakke kan cewa ko tianshin ne suke sayarwa ba. Neman kudi na iya sanyawa a jika wa mutane a ji-garau. Kuma ina kira ga ma’aikatar lafiya ta tarayya da gwamnatocin jihohin Arewa, su gudanar da bincike kan masu tallar magunguna barkatai. Idan har kowa zai sayi maganin Bature ko na gargajiya ya sha a titi, to ina amfanin zuwa wajen Likita? Wajibi ne a tursasa ’yan matan Abuja masu tianshi, su nuna hujjar amincewar NAFDAC da ma’aikatar lafiya ta tarayya. Daga Mus’ab Kamaluddeen, Abuja.

Sakonnin waya

’Yan tsiraru ne ba mutanen Zariya ba
Mutanen Zaria  masu hankali da Sanin ya kamata ne.  A siyasa ba ma hauka, domin an ta bi ana ta yadawa a gari cewa wai talakawan gari mun zane  dan majalisa mai wakiltarmu a majalisar tarayya (Dokta Abbas Tajuddeen), saboda wai ba ya taimakon al’umma, kuma ba ya ziyartar mazabar tasa, to karya ne! Ba haka ba  ne. Wadanda suka shirya wannan abu  ’yan tsiraru ne. Daga Basheer Mukhtar Yusuf Zaria. 07034514844

Ga Gwamna Wamako
Aminiya don Allah ku isar da kukanmu zuwa ga Gwamnan Sakkwato, Magatakarda Wammako, mun ji aikin da yake yi, ya gyara wasu yankuna na kananan hukumomin Jihar, amma an mayar da yankin Gada ta Gabas saniyar ware. Idan damina ta sauka ya fi sauki ka je Legas da ka je Gada zuwa Kaffe. Don Allah a duba, a gyara mana hanya. Daga Garba Mazaunin Fatakwal 08054769251.

Adalci tushen zaman lafiya
Edita don Allah ka gaya wa al’ummar Najeriya adalci shi ne tushen zaman lafiya. Adalci a amsalalci; adalci a Coci; adalci a wuraren aiki. Adalci ne igiyar gwajin tushen dokar ginin Najeriya. Daga B. A. Gayya 07088028856. Mai gado street Sabon Gari Zariya.

Jaje ga wakilin Malumfashi da kafur
Jaje Babangida Ibrahim Mahuta Talau dan majalisar tarayyata mai wakilar Malumfashi da kafur jaje akan dukan da ya sha a wurin daurin auren ’yar tsohon shugaban majalisa, Alhaji Aminu Bello Masari. Shawarata ga Babangida Ibrahim Mahuta Talau, ita ce ya rika taimakon matasa, don su ne suka yi tsayin da ka kai ga darewa kujerar da kake. Daga Kabir Sakaina. [email protected]  

Ina adamu Akuyam?
Aminiya muna neman abokinmu Adamu Magaji Akuyam, Jihar Bauchi, tunda muka gama Kaduna Poly (Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna) a shekarar 1987, ba mu sake haduwa ba. Daga Abba Isa da Ahmad Habibu Yadakwari. 08109184156.

Ga Sarkin Yakin Hausa
Gwamna Shema ka dubi jama’ar Filin Polo da idon rahama, a yi musu hanya, ka tuna fa kai nasu ne, su naka ne. Don kai ka samar da wutar lantarki a  Unguwar mai nagarta, ka taimaka karka barmu cikin rudu Sarkin Yakin Hausa. Daga 08032846844.

Kantomomin Kano na sayen gonaki
An ki cin biri, an ci dila tsantseni a Kano Kantomomi na ta sayen gonaki da filayen talakawa. Daga Hamza Gwarzo. 07059914018.

Tambaya ga Adam A. Zango
Salam. Edita ga sako gareka da Adam A. Zango, ba ni manta da fim dinsa da ya sani zubar da hawaye, wanda ya baiwa kurma, kuma makaho ajiyar kudi; ya zo ya samu kudin. Don Allah Edita ka samo mana Zango Kudi ya samu sun ishe shi ko rashinsu ne ko gajiya yayi da fadakarwa? Nagode Daga Maikaunarsa, Hassan Ali Akurba Jiahr Nasarawa 08086610494.

A kara filin sakonni
Shazwara ga filin sakonni, don Allah aminiyata in da hali a kara filin, don yana kara wa Aminiya farin jini. A kara don kowa ya tura sakonsa so yake ya saya, ya gani. Daga M.D. Sani Bararo Kano Hausawa 08038492252.

Ina lambar agajin ’Yan sanda?
A ofishin ’yan sanda na C.P.S da ke Funtuwa na je neman lambar da ake kiran su idan ana neman taimakon gaggawa , don muna fama da ’yan sace-sace, amma abin takaici shi ne, daukacin ’yan sandan ba su san lambar ba, sai kame-kame, wai sai na ga D.P.O, domin shi kadai ne yasan lambar. A gaskiya hakan abin kunya ne ga rundunar ’yan sandan Najeriya. Daga Isah Abdussalam Unguwar Wanzamai Funtua.

Ga Gwamnatin Jigawa
Gwamnatin Jigawa mai adalci, ki gyara mana hanyarmu daga Kazaure zuwa Roni. Kuma a mika min godiya ga Gwmanan Talakawa Sule Lamido, Allah Ya kare mana kai. Amin summa.amin. Daga Sani I. Roni 07069744327.

Ga Gwamnatin Kano
Gwamnatin Kano ya kamata a yi wani tsari don bai wa jama’a masu abin hawa damar kai ’ya’yansu makaranta ko iyali asibiti a kan babur. Domin wannan doka ta jefa karatun yara da hidimar iyali cikin wani mawuyacin hali. Idan dai mulki don talaka ake yi, lokaci ya yi da za a yi nazari kan wannan matsalar. Daga Usman PPA 08065794538.

Romon dimokuradiyyar Zamfarawa
Idan har kuna son romon dimokuradiyya, Zamfara ku tsayar da Bashir Adamu IMAD a matsayin dan takarar Gwamnanku a shekarar 2015. Daga Muhammad Ahmad 08036919511.

Tunatarwa
Daga Sa’ad Bin Abi Wakkas, Allah Ya yarda da shi, cewa, Manzon Allah (SAW) yana fada: “Abubuwa hudu suna daga cikin kwnaciyar hankali; mata tagari da gida mai yalwa da makwabci nagari da abin hawa lafiyayye.” Ibn Hibban. Allah Ya sa mu dace. Daga Fatima Saddik Sidi Kabara 07051757239.

Ga Sheikh dahiru Bauchi
Salam. Editan Amintacciyar Aminiya, don Allah ka isar min da sakona ga Sheikh dahiru Usman Bauchi “Fa’inni Mustapha uhibbuka hubba la yazalu wala yafna Habibuka Mustapha yarju sa’adatan bi barhama sirri! Sirri! sirril wulayti! Daga 08036968509.

Ga Giwar danmajen Kano
Edita don Allah ka ba ni dama in yi murna wurin Gimbiya Sa’adiya Ado bayero (diya mai kamar uwa), bisa ga nadin sarautar da aka yi mata, ta Giwar danmajen Kano a dalilin hakurinta da biyayayr aure. Allah Ya taya ki riko. Amin. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.