Tifa ta hallaka mutum tara a Gora
A ranar Alhamis da ta gabata ne al’ummar garin Gora da ke karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa suka kwana cikin alhini sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara tare da jikkata wasu da dama. Lamarin ya auku ne da misalin karfe 9:30 na dare lokacin da wata tifa shake […]
A ranar Alhamis da ta gabata ne al’ummar garin Gora da ke karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa suka kwana cikin alhini sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara tare da jikkata wasu da dama.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 9:30 na dare lokacin da wata tifa shake da yashi ta saki hanya ta yi kan dafifin mutanen da ke bakin hanya sakamakon tare hanya da aka ce ’yan fashi sun yi a yankin, inda tifar ta tattake mutanen.
Wakilinmu ya gano cewa mutum shida daga cikin tara da suka rasu a hadarin, ’yan garin na Gora ne yayin da uku baki ne mazauna yankin kuma galibinsu matasa ne ’yan kasa da shekara 30.
daya daga cikin wadanda hadarin ya auku a kan idonsu kuma hudu daga cikin wadanda suka rasu mutanen gidansu ne, Malam Lawal Tanko ya shaida wa ce wakilimu cewa:
“Da misalin karfe tara da rabi na dare ne muka samu labarin cewa wasu ’yan fashi sun tare hanya a kusa da Tudun Wada mai tazarar kilomita biyu zuwa uku yamma da garinmu, hakan ya sa matasa suka yi dandazo a gefen titi domin sanar da matafiya gudun kada su auka cikin ’yan fashin. Mun yi sa’ar tsayar da motoci da dama, daga baya sai ga wannan tifa kirar Mark ta kwararo a guje inda matasan suka yi kokarin tsayar da ita. Kafin mun ankara sai tifar ta saki hanya ta fara tattake mutane, daga nan ta je ta daki bayar wata mota Sharon sannan ta tafi gefe ta fadi.”
Malam Lawan ya ce, bayan faduwar tifar da suka bincika sai suka tarar da gawarwakin matasa tara da ta kashe kuma baki dayansu maza ne ’yan kimanin shekara 25, ciki har da wani fitacce a yankin mai suna Alhaji Kabiru K.B mai gidan bulo.
Zuwa hada wannan rahoto, an nemi direban tifar sama da kasa an rasa, kamar yadda aka gaza gano mamallakin tifar.
Babban Jami’in ’Yan sandan yankin, CSP Ibrahim Adamu ya tabbatar da uakuwar lamarin. Kuma an yi jana’izar wadanda suka rasu washegari Juma’a kamar yanda addinin Musulunci ya tanada saboda dukkansu Musulmi ne.