Tifa ta take magidanci da iyalansa 6 a Zamfara

Wani magidanci da iyalansa su shida sun rasu bayan da wani direban tifa ya bi ta kansu da mota a garin Gusau, fadar Jihar Zamfara.

Tifa ta take magidanci da iyalansa 6 a Zamfara

Wata motar daukar kaya ta fadi

Wani magidanci da iyalansa su shida sun rasu bayan da wani direban tifa ya bi ta kansu da mota a garin Gusau, fadar Jihar Zamfara.

Aminiya ta gano cewa tifar ta kwace wa direbanta ne a kusa da Gusau Otel a ranar Litinin, ta bi ta kan magidancin da matarsa da ’yayansu hudu suka ce ga garinku nan

A cewar wani wanda ya shaida afkuwar lamarin ya ce da iyalinsa su shida suna kan babur din ne zai kai su unguwa sai motar ta kwace wa direba kuma ta bi ta kansu suka sheka Lahira.

“Ga alama ma dai tifar ba ta da cikakken burki domin kasan mafiya yawan tifofin nan ba su da cikakken burki.

“A gaskiya da direban yana da cikakken burki zai iya tsayar da motar tun kafin ta kai ga hallaka magidancin da iyalansa.

“A gaskiya wannan hadarin abu ne mai tayar da hankali gaya, domin ganin gawarwakin magidancin tare da iyalansa su shida abu ne mai ban tausayi sosai.

“A lokacin da na isa kan gawarwakin magindacin da iyalansa sai da na zubar da kwalla don tausayi, musamman lokacin da na ga gawarwakin nasu yashe a gefen titi,” in ji wanda ya shaida afkuwar lamarin.

Kakakin Rundunar Yan Sanda ta Jihar Zamfara, Sufritanda Yazid Abubakar ya tabbatar da rasuwar Mutane Shida a sakamakon hadarin.

Ya ce “Ba shakka mun sami labarin faruwar wannan hadarin mota inda wani mai tifa ya bi ta kan wani magidanci wanda ke dauke da iyalansa a kan babur kuma sakamakon haka magidancin da iyalan nasa su shida suka rasa rayukansu.

“Direban tifar a yanzu haka yana hannunmu kuma muna ci gaba da binciken domin gano yadda wannan al’amari mara dadi ya faru.

“Da zarar mun kammala binkice za mu bayyana sakamakon binkicen ga al’umma domin sanin cikakken bayanin yadda lamarin ya afku,” in ji jami’in.

v