Tiger Woods ya koma na 104 a duniya
A karon farko tun a shekarar 1996, shahararren dan kwallon Gwaf (Golf) Tiger Woods ya samu koma baya mafi muni a tarihinsa inda yanzu haka ya koma matsayi na 104 a jerin ’yan kwallon gwaf da suka fi shahara a duniya. dan shekara 39, Woods, wanda ya lashe gasar kwallon gwaf ta duniya har sau […]
A karon farko tun a shekarar 1996, shahararren dan kwallon Gwaf (Golf) Tiger Woods ya samu koma baya mafi muni a tarihinsa inda yanzu haka ya koma matsayi na 104 a jerin ’yan kwallon gwaf da suka fi shahara a duniya.
dan shekara 39, Woods, wanda ya lashe gasar kwallon gwaf ta duniya har sau 14 a lokuta daban-daban ya koma na 104 a wani jadawali da wata mujalla da ake bugawa a Amurka ta fitar a watan jiya, (Maris, 2015).
Tiger Wood, dan asalin Amurka ya fara zama zakaran duniya a kwallon gwaf ne a shekarar 1997 inda ya shafe kimanin makwanni 683 yana rike da kambun gwarzon dan kwallon gwaf na duniya tarihin da babu wani dan kwallon gwaf da ya taba samun haka kawo yanzu, sai ga shi ya koma na 104.
Tun cikin shekarar 2008 ne dai tauraruwarsa ta yi kasa sai dai ya samu nasarar lashe wasu kofuna a shekarar 2013.
Ko watan Fabrairun wannan shekara Tiger Woods sai da ya janye daga wata gasa ta kwallon gwaf ta duniya da ake wa lakabi da Famer’s Open saboda matsalar ciwon baya.
Matsaloli da yawa ne suka yi wa dan kwallon gwaf din katutu da suka hada da ciwon baya, al’amarin da ya sa yake daukar tsawon lokaci ba tare da ya shiga gasar kwallon gwaf ta duniya a sassan duniya ba.
Sai dai dan kwallon ya nuna aniyarsa ta halartar gasar kwallon gwaf ta duniya da za a yi a Amurka (US Masters) a makon gobe idan ya murmure.