Tijjani Baban Shadda ya rasu
Allah ya yi rasuwa ga fitaccen dan kasuwar nan da ke Bauchi Alhaji Tijjani Baban Shadda, sakamakon bugun zuciya lokacin da ya samu labarin rasuwar yayansa Alhaji Wada Abdullahi wanda ya rasu a hadarin mota a ranar Litinin a hanyarsa ta zuwa Gombe.Tijjani Baban Shadda ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya takwas. Ya […]
Allah ya yi rasuwa ga fitaccen dan kasuwar nan da ke Bauchi Alhaji Tijjani Baban Shadda, sakamakon bugun zuciya lokacin da ya samu labarin rasuwar yayansa Alhaji Wada Abdullahi wanda ya rasu a hadarin mota a ranar Litinin a hanyarsa ta zuwa Gombe.
Tijjani Baban Shadda ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya takwas. Ya rasu yana da shekara 55 a duniya. An haifi marigayin ne a Unguwar kofar Ran da ke cikin garin Bauchi, kuma shi da yayansa Alhaji Wada sun ba da gudunmawa wajen bunkasa harkokin kasuwanci a garin Bauchi tab yadda za a dade ana tunawa da su.