Tijjani Usman Bello, a Maiduguri.
Ana zargin wata mata mai suna Nkechi Isioko, da ke kauyen Mpu, karamar Hukumar Aninri da ke Jihar Enugu da yunkurin sayar da jarirnta kan kudi Naira dubu 100 ga wata mace da ake kyautata zaton tana fataucin yara kanana mai suna Blessing Egbo. Bayanin da Aminiya ta samu shi ne, matan biyu suna cikin […]
Ana zargin wata mata mai suna Nkechi Isioko, da ke kauyen Mpu, karamar Hukumar Aninri da ke Jihar Enugu da yunkurin sayar da jarirnta kan kudi Naira dubu 100 ga wata mace da ake kyautata zaton tana fataucin yara kanana mai suna Blessing Egbo.
Bayanin da Aminiya ta samu shi ne, matan biyu suna cikin kammala kulla cinikin ne sai jami’an tsaro na Cibil Defence suka yi masu dirar mikiya, suka kama su.
Nkechi, uwar yaron da za ta sayar da dan nata, ta shaida wa jami’an tsaron cewa Blessing Egbo ta fara kawo mata Naira dubu goma, kafin alkalamin ciniki, a lokacin da ta kawo cikon Naira dubu 90 sai jami’an tsaron suka cafke su.
Da aka tambayi Nkechi Isioko dalilin da ya sa za ta sayar da dan nata sai ta ce: “Ina so ne in kula da lafiyata, sauran canjin kuma in rika cin abinci da su.”
Da yake yi wa manema labarai karin bayanin yadda asirin masu laifin ya tonu, Kwamandan Hukumar Tsaro ta Cibil Defence na Jihar Enugu, Lar Stephen Zwali, ya gargadi duk masu mugun hali da su kuka da kansu, domin hukuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kama su, ta mika su kotu.