Tijjaniyyah ta nada Sanusi II a matsayin Khalifanta na Najeriya
Sanusi II ya zama Halifan Tijjaniyyah kasa da shekara daya bayan tube shi daga sarautar Kano
An nada tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon shugaban Darikar Tijjaniya na Najeriya.
An sanar da nadin ne yayin taron Darikar Tijjaniya da yake gudana a Sakkwato, wanda Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal suke daga cikin mahalarta.
- Shekara 5 bayan rabuwarsu, ta dawo gidan tsohon mijinta ta casa amaryarsa
- An rufe makarantar da ‘yan bindiga suka kwashi dalibai a Kaduna
Tun bayan rasuwar Sheikh Isyaka Rabi’u wanda ke rike da kujerar a baya, kungiyar ba ta nada magajinsa ba sai yanzu da ta nada tsohon Sarkin.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, wanda kaka ne ga Sanusi II, shi ma ya taba rike halifancin darikar.
Nadin Sanusi II a Halifancin Tijjaniyyah na zuwa ne kasa da shekara daya bayan Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tube shi daga sarautar Kano.
Darikar Tijjaniya na da miliyoyin mabiya a kasashen Morocco da Algeria da kasashen Afirka ta Yamma musamman a Senegal, Gambia, Mauritania, Mali, Guinea, Nijar, Chad, Ghana, Najeriya da kuma Sudan.