TikTok ya daina aiki a Amurka
Donald Trump ya ce akwai yiwuwar ya ƙara tsawaita amfani da manhajar TikTok zuwa kwanaki 90.
Tiktok ya daina aiki a Amurka, yayin da dokar da hukumomin ƙasar suka sa ta dakatar da manhajar daga ranar 19 ga watan Janairu, 2025 ta fara aiki.
Tun a yammacin ranar Asabar ne, Amurkawa suka fara fuskantar matsala wajen shiga manhajar TikTok, sa’o’i kafin aiwatar da matakin ya daina aiki a ƙasar.
Ma’abota manhajar kimanin miliyan 170 a Amurka sun yi ta samun sakonnin cewa, an dakatar da manhajar na ɗan wani lokaci.
Dama TikTok ɗin ya bayyana cewa zai daina aiki a Amurka daga wannan Lahadin idan har gwamnatin Shugaba Joe Biden ba ta ɗauki matakin hana dakatar da shi ba.
Amurkan dai ta ce za ta ɗauki matakin dakatar da manhajar idan har kamfanin ByteDance mallakin manhajar ya ki siyar wa Amurka.
Sai dai Shugaba mai jiran gado, Donald Trump ya ce akwai yiwuwar ya ƙara tsawaita amfani da manhajar zuwa kwanaki 90 idan ya sha rantsuwar kama aiki.
A watan Afirilun bara ne dai, shugaba Joe Biden ya yanke hukuncin hana amfani da manhajar ko siyar da ita, wanda majalisar dokokin kasar ta amince da shi bisa dalilai na tsaro.
’Yan majalisar dai na fargabar China ka iya amfani da manhajar wajen samun bayanan Amurkawa domin ta yi amfani da su wajen yaɗa manufofinta na siyasa.