TikTok ya dawo aiki a Amurka
TikTok ya dawo aiki a Amurka bayan wani ɗan lokaci da aka sanar da dakatar da amfani da manhajar a ƙasar. Manhajar TikTok wadda ta China ce, ta gode wa Shugaban Amurka da za a rantsar a yau Litinin, Donald Trump, wanda ya ce zai yi ƙokari ya warware batun da ya jawo matsalar tun […]
TikTok ya dawo aiki a Amurka bayan wani ɗan lokaci da aka sanar da dakatar da amfani da manhajar a ƙasar.
Manhajar TikTok wadda ta China ce, ta gode wa Shugaban Amurka da za a rantsar a yau Litinin, Donald Trump, wanda ya ce zai yi ƙokari ya warware batun da ya jawo matsalar tun a farko.
Kamfanin ya ce zai yi aiki tare da Trump domin samar da mafita ta dogon lokaci don ci gaba da kasancewa a Amurka.
Bayanai sun ce kamfanin Bytedance da ya mallaki TikTok ya musanta zargin satar bayanai yana bai wa China, kuma ya ɗauki wasu matakai don nuna hakan, ciki har da mayar da shalkwatar kamfanin zuwa Singapore.
Tun da farko, Mista Trump ya ce zai ba da umarnin zartarwa da ya hau kan karagar mulki a yau domin ba TikTok damar ci gaba da aiki a Amurka.
Haka kuma, Trump ya ce yana shirin fitar da wata dokar da za ta bai wa TikTok damar neman wani wanda Amurka ta amince da shi da zai saye kamfanin kafin dokar haramcin ta fara aiki gadan-gadan.
Ya bayyana wannan matsayar da ke da dangantaka da manhajar shi ta Truth Social, yayin da miliyoyin Amurkawa masu amfani da manhajar suka wayi gari Lahadi adireshinsu na TikTok sun daina aiki.
A watan Afirilun bara ne dai, shugaba Joe Biden ya yanke hukuncin hana amfani da manhajar ko siyar da ita, wanda majalisar dokokin kasar ta amince da shi bisa dalilai na tsaro.
’Yan majalisar dai na fargabar China ka iya amfani da manhajar wajen samun bayanan Amurkawa domin ta yi amfani da su wajen yaɗa manufofinta na siyasa.