Tilas a magance matsalar coge a cikin kasafin kudi
“Coge shi ne a sanya wani abu a cikin wani abu da niyyar gamsar da kai ko a boye wani bayani.” Wannan shi ne ma’anar da dan Majalisar Wakilai daga mazabata ta Toro Alhaji Lawal Yahaya Gumau ya bai wa kalmar nan ta Padding da ake zargin shugabannin majalisar da yi a kan kasafin kudin […]
“Coge shi ne a sanya wani abu a cikin wani abu da niyyar gamsar da kai ko a boye wani bayani.” Wannan shi ne ma’anar da dan Majalisar Wakilai daga mazabata ta Toro Alhaji Lawal Yahaya Gumau ya bai wa kalmar nan ta Padding da ake zargin shugabannin majalisar da yi a kan kasafin kudin bana. Ni ma kuma na amince da wannan ma’ana.
Wannan kalma ta coge (padding) a cikin kasafin kudi, Majalisar Dattawa ce ta fara amfani da ita a daidai lokacin da takaddama take da zafi-zafi a tsakanin majalisar da Fadar Shugaban kasa. Majalisar ta yi zargin an sace gangariyar kwafen kasafin da Shugaba Muhammadu Buhari ya aike mata don yin muhawara tare da amincewa da shi, kuma an kawo wanda aka yi coge a ciki, an yi ta cece-ku-ce kan wannan lamari na tsawon lokaci. A lokacin da ake waccan muhawara Shugaban Majalisar Wakilai Honorabul Yakubu Dogara ya ce, su a majalisarsu suna da gangariyar kwafen kasafin na bana, har ma ya nuna wasan yara ne a ce kundin kasafin ya bace.
Bayan maganar ta kwanta kwatsam a makon jiya sai batun ya gangaro Majalisar Wakilai sakamakon cire Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar wato Alhaji Abdulmumini Jibrin daga mukaminsa. Sai rikici ya barke a majalisar sakamakon zargin da Abdulmumini Jibrin ya yi cewa Shugaban Majalisar da mukarrabansa uku sun yi cogen da ya kai na Naira biliyan 40 a kasafin kudin bana.
dan majalisar, ya kuma ce an sauke shi daga mukaminsa ne saboda yana adawa da shirin kafa dokar da za ta ba da rigar-kariya ga shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa wato Majalisar Wakilai da ta Dattawa.
Har wa yau Abdulmumini Jibrin ya shaida wa duniya cewa “Ina da shaidun da ke nuna cewa Dogara da mataimakinsa Yusuf Lasun da Alhassan Doguwa (Babban Mai tsawatarwa) da Leo Ogor (Shugaban Marasa Rinjaye) sun ware wa kansu Naira biliyan 40 daga cikin Naira biliyan 100 da aka ware wa majalisar.
Daga farko Shugaban Kwamitin Watsa Labarai na Majalisar, Abdulrazak Namdas, ya musanta zarge-zargen da Jibrin ya yi, inda ya ce zafin cire shi da aka yi daga mukamin shugaban kwamitin kasafin kudi ne ke damunsa.
Wannan batu na coge a kasafin ya ci gaba da jawo ka-ce-na-ce a kasar nan na tsawon mako biyu a yanzu, inda har wadansu daga cikin ’yan majalisar irin su Alhaji Lawal Yahaya Gumau suka fara kiran a gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar lamarin.
A hirarsa da gidan talabijin na Channels Tb a Abuja a ranar Alhamis din makon jiya, Lawal Gumau ya bayyana cewa tun shigarsa majalisar a shekarar 2011 ya iske ana yin coge a cikin kasafin kudi, kuma da ya nuna bai kamata haka ya ci gaba da faruwa ba, sai aka nuna masa hakan ba zai yiwu ba. “Na zo Majalisar Dokoki ta kasa a shekarar 2011 kuma na yi ta fada kan yadda ake coge a cikin kasafi tun shekarar 2012, duk shekara sai an yi coge. Babu wanda zai ce ba a yin coge. Ya kamata mu fara bincike a kai, kuma duk wanda ya bincika zai ga ana yin wannan coge.”
Honorabul Lawal Gumau ya bayyana dalla-dallar yadda ake yin wannan coge da cewa: “Bayan kasafin kudi daga kwamitoci ya isa kwamitin kasafi za su yi aiki a kan kasafin. Bayan sun yi aiki a kansa, kwamitin zai dawo da shi ga zauren majalisa inda za a karanta shi a samu matsaya a kai. To da zarar majalisa ta amince da shi kafin a mika shi ga Shugaban kasa ne ake sanya cogen, to a wannan wuri ne cogen ke shigowa. Shugaban kasa ba zai san cewa wannan aiki ba ya cikin kasafin da wakilan majalisa suka amince da shi ba, haka Shugaban kasa zai sanya hannun amincewa da shi. Su ma sauran ’yan majalisa ba za su san bayan sun amince da kasafi an sanya wani abu a ciki ba. Don haka abin da muke cewa shi ne, lokacin da suka dawo da kasafin da aka amince da shi (aka sanya masa hannu), to a nan ne sauran ’yan majalisa za su san an shigar da wani kari a kan abin da muka amince da shi.”
Ana cikin wannan dambarwa ne Jam’iyyar APC ta kasa ta gayyaci Jibrin a ranar Talata, kila a tuhume shi da kokarin jefa majalisar a cikin rudu, musamman ganin shugabanta Yakubu Dogara yana ‘biyayya ga jam’iyya.’ To amma abin da muke son shaida wa Jam’iyyar APC da duk masu kaunar kasar nan, shi ne lallai wannan matsala ya wajaba a tsaya a yi mata binciken kwakwaf. Bai kamata a wannan lokaci da yaki da almundahana ke cikin manyan shika-shikan gwamnatin APC a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ba, a ce wannan muguwar dabi’a ta satar kudin jama’a a fakaice ta ci gaba.
Mun ga yadda Shugaba Buhari ya ki sanya hannu a kan kasafin kudin bana na dogon lokaci saboda irin wannan coge da aka yi a wurare da dama a cikin kasafin da aka ce sun kai har 2000. A lokacin mutane da dama sun yi ta ganin laifinsa kan ya ki amincewa ya sanya hannu a kan kasafin, to amma da yake Allah ba azzalumi ba ne ga shi ko wata uku ba a cika ba, cogen da ya jawo ya ki sa hannu a kasafin ya fara bayyana.
Yaki da cin hanci da rashawa da almundahana da cuwa-cuwa da coge da aringizo da babakere da rub-da-ciki a kan dukiyar talakawa yaki ne da yake bukatar sadaukar da kai da tsoron Allah daga dukkanmu. Duk wanda ya yi ba daidai ba, a yi masa ba daidai ba.
An dade ana coge iri-iri a kasar nan, musamman a kan kasafin kudi, misali an sha zargin ’yan majalisa musamman ta Dattawa da kara kudi a kan kasafin ma’aikatu da hukumomin gwamnati, amma su ne za su cire kudin su raba a tsakaninsu. An sha zargin ’yan Majalisar Dattawa da ta Wakilai da zuwa ma’aikatu suna karbar kudi da sunan duba ayyukansu. Ya kamata wannan gwamnati ta APC ta tsaya tsayin-daka wajen ganin gwamnatin Buhari ta samu nasara a yakin da take yi da almundhana da coge da cuwa-cuwa da cin hanci da rashawa koda hakan zai shafi ’ya’yanta. Yanzu ne lokacin da za a dora Najeriya a kan turba ta gaskiya da rikon amana, bayan dogon lokacin da aka dauka ana wa-ka-ci-ka-tashi da dukiyar kasar nan. Wannan matsala bat a Jibrin da Dogara ba ce, matsala ce ta gyaran kasa da tsabtace ta daga dagwalon da aka sanya ta a ciki shekara da shekaru.
Fallashe-fallashen da aka rika yi kan yadda jami’an gwamnati suka mayar da dukiyar gwamnati tamkar ganima suka tatuke aljihun gwamnati suka talautar da kasar nan, suka jefa jama’a a cikin kuncin rayuwa, bai kamata a yanzu wani ko wadansu mutane su yi kokarin rufa asirin irin wadannan mabarnata ba.
Don haka ni Gizago ba na goyon bayan yunkurin da duk wani ko wadansu za su yi don yi rufa-rufa game da wannan batu na coge. Tunda majalisar ta kwance kunshin barnar da ake tafkawa a bainar jama’a, kuma har ta kai manyan aktocin da suke fage sun zargi juna da yin cogen, har babban akta ya rubuta wa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFCC da ICPC da hukumomin tsaro takardun korafi kan badakalar, wajibi ne a bar su su yi aikinsu na bincike da hukunta duk masu hannu a ciki. Tuni dai majalisa ta ce aikin Alkarya Fina-Finai na daga cikin ayyukan da aka yi cogensu, yayin da Jibrin ya ce Dogara ya karkatar da wani aikin ruwa zuwa gonarsa a Jihar Nasarawa.
Don haka EFCC da ICPC da ’yan sanda da DSS da lauyoyi da alkalai da kungiyoyin kare hakkin jama’a da ’yan siyasa musamman ’yan adawa da kafafen watsa labarai da daukacin jama’ar Najeriya, wannan babban kalubale ne gare ku.