Tilas mu nemo wa Arewa alkibla yanzu
A gaskiyar magana ya kamata sabuwar majalisar karo ta 9 ta fito da wani tsari da kowanne dan Majalisar Dattawa da na Wakilai da ’yan majalisar jihohi zai iya ganawa da al’ummar mazabarsa kai-tsaye, domin tattaunawa kan abin da ya kamata ya mika ga majalisa a matsayin ra’ayin al’ummarsa. Kuma lallai kudin nan da ake cewa […]
A gaskiyar magana ya kamata sabuwar majalisar karo ta 9 ta fito da wani tsari da kowanne dan Majalisar Dattawa da na Wakilai da ’yan majalisar jihohi zai iya ganawa da al’ummar mazabarsa kai-tsaye, domin tattaunawa kan abin da ya kamata ya mika ga majalisa a matsayin ra’ayin al’ummarsa.
Kuma lallai kudin nan da ake cewa na aikin mazabu da ake ba wa ’yan majalisa miliyoyi Naira akalla ana kashe kaso biyu cikin uku na wadannan kudade a cikin mazabar da wakili ya fito. Hakika hakan zai magance ko ya rage matsalolin ilimi da talauci da inganta kiwon lafiya a kasar nan, domin ko’ina za su samu ayyukan alheri kuma al’umma za su gamsu cewa lallai akwai wani abu da ake kira romon dimokyradiyya. Kowanne sanata an ce ana ba shi sama da Naira miliyan 13 a matsayin kudin inganta mazabu, ban da alawus da albashi. Dan Majalisar Wakilai ana ba shi sama da Naira miliyan 10 su kuma ’yan majalisar jihohi na karbar Naira miliyan bakwai a kowane wata.
Wani abin takaici in ba a yi hankali ba majalisa ta 9, tana iya fin ta baya lalacewa, domin yanzu ga rigimar shugabanci a majalisa, wanda sababbin da suka je har an fara ba su toshiyar baki, domin su yarda da shugabancin wani. Wannan zai sa a fara koya musu karbar na goro, in sun yi magana ko sun ki yarda a ce to shi ke nan sai dai su zama ’yan kallo, ba za a rika yi da su ba.
Lallai Shugaban Kasa ya san hanyoyin da zai bi domin yakar wannan bakar al’ada a majalisun kasar nan.
Kuma ya kamata lallai a san yadda za a yi a gyara kundin tsarin mulkin kasar nan ya zama duk wani zababbe kada ya wuce zango daya, ma’ana ya zama da ya yi shekara biyar to ya kauce ya ba wa wadansu dama, ya alla Shugaban Kasa ne ko gwamnoni da ’yan majalisa. Wannan zai rage hadamar neman mulki da wadansu tsirari ke hana a dama da wadansu, kuma wannan zai rage siyasar kudi da ta ubangida, ya rage rikicin siyasa da banga, kuma hakan zai taimaka a samu ayyuka suna tafiya yadda ya kamata. Kowa zai yi kokari ya yi abin kirki kafin lokacinsa ya kare ba tare da barin kwantan aiki ba.
Kuma gaskiya al’umma sun gaji da tsarin mulkin nan na Amurka, mutane yanzu sun fi son a koma tsarin mulki irin na kasar Birtaniya, shi ne tsari da yake daidai da al’adun mutanenmu, kuma akwai tattalin dukiyar kasa ba tare da al’mubazzaranci ba. Muna sa ran wannan majalisa ta 9 za ta jajirce domin dawo da wancan tsarin da aka fara da shi a farkon samun mulki kai, babu laifi a yi masa gyara yadda zai biya bukatun ’yan kasa. Amma lallai majalisa ta zama ana zama ne na wucin-gadi. Hakan zai taimaka wa talakawa su zama suna ganawa da wakilansu ba tare da wasan buya ba.
Wannan karon muna sa ran majalisa ta 9 za ta fito da tsarin aiki da dokoki yadda ya kamata kuma dokoki masu tsauri da nuna ba sani ba sabo, wannan shi ne zai magance matsalar cin hanci da rashawa da zalunci ko daure wa karya gindi a kasar nan. Kuma ya zama dole a yi wani gyaran fuska a bangaren shari’a da bangaren tsaro yadda kwalliya za ta rika biyan kudin sabulu.
Haka muna sa ran wannan majalisa ta 9 za ta yi kokari ta dawo wa kananan hukumomi martabarsu a rika ba su kudadensu kai-tsaye maimakon yanzu da gwamnonin jihohi suke yi musu karfa-karfa. Wannan zai taimaka wa al’umma na can kasa su san ana dimokuradiyya ta hanyar samar da ayyukan yau da kullum kuma ana samar musu da aikin yi da bunkasa ababen more rayuwa a tsakanin al’umma musamman a karkara, amma ya zama ana sa ido sosai.
Sannan lallai Shugaban Kasa ya yi kokari ya zabo abokan aiki jajirtattu ban da la’akari da abokantaka ko ’yan uwantaka ko surkuntaka ko takama da asali. A dubi cancanta da nagarta da karancin buri da kishin kasa da kwazon aiki. Kuma wannan karon Shugaban Kasa da ’yan majalisa da gwamnonin jihohi su ba da muhimmanci a kan tsaro da ilimi da harkar lafiya da bunkasa tattalin arziki ka’in-da-na’in, kada kuma a rika sakaci ko jan kafa wajen abin da ya shafi bukatun al’ummar kasa musamman kasafin kudi da abin da ya shafi ababan more rayuwa.
Akwai wani shiri da Shugaban Kasa ya bijiro da shi mai taken (Change Begin With Me) wanda gwamnonin jihohi suka yi masa rikon sakainar kashi, Shugaban Kasa kuma ba ya bibiya sai dai talla a kafafan watsa labarai musamman talabijin. Lallai wannan karo a ba wa wannan shiri karfi sosai domin cusa tarbiyya da kishin kasa da gaskiya a zukatan jama’a.
Kuma Shugaban Kasa a wannan zango na karshe, ya dubi Arewa da idon rahama, ya ingantata ta fuskar hadin kai da zaman lafiya da bunkasa tattalin arziki da kasuwanci da inganta ilimi a Arewa, domin wadannan su ne ajandar Arewa. Kuma hatta man fetur an tabbatar akwai shi a jihohi 3 na Arewa, to a wadannan shekara hudu da suka rage wa Shugaba Buhari ya tabbatar an fara cin gajiyarsu da batun jawo ruwan nan zuwa Arewa, domin wankin hula yana neman ya kai mu ga dare. Sannan a ba wa jihohi dama su samar da wutar lantarki a kan wacce ake samu daga Gwamnatin Tarayya ta zama da araha. Kuma ya kamata mu tambayi kawunanmu,wane dalili ne ya sa Arewa ta ja ragamar kasar nan karo na 9 amma har yanzu Arewar na fama da talauci da jahilci da tashe-tashen hankula da rashin hadin kai? Lallai a wannan karon ana bin Shugaban Kasa da duk wani dan siyasa zababbe na Arewa da sarakunan gargajiya da ’yan boko da masu fada-a-ji da malaman addinai bashi. Ya zama kalubale ko dai a zo a samar wa Arewa mafita ko in mulki ya koma Kudu za a zuba wa ’yan Arewa ido suna ta kashe kawunansu a banza a yi ta samar da karin marayu da sauran masu aikata laifuffuka.
Lallai ne shugabanni da masu ruwa-da- tsaki a Arewa su samar da hanyoyin da za a bi a bunkasa arziki da zaman lafiya da zamantakewa mai inganci. Dole shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya da ’yan boko da masu hali da malaman addinai da masu fada-a-ji su nemo yadda za a gudu tare a tsira tare ko Arewa ta samu ta dawo da martabar da aka santa da ita ta fuskar hadin kai da zaman lafiya da karuwar arziki da tarbiyya.
Daga Abdullahi Idris Yakasai
08054407095
Email: [email protected]