Tilas Musulmi su hada kai saboda barazanar makiya – Liman
daya daga cikin Limaman Jumu’a da Idi a Jihar Yobe, Ustaz Babagana Malam Kyari ya ce hadin kan al’ummar Musulmi ya zama wajibi a wannan lokaci da Musulmin suka zama kamar mikiya a cikin tsuntsaye, inda makiya addinin suka taso su a gaba.Ustaz Babagana Malam Kyari ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya a […]
daya daga cikin Limaman Jumu’a da Idi a Jihar Yobe, Ustaz Babagana Malam Kyari ya ce hadin kan al’ummar Musulmi ya zama wajibi a wannan lokaci da Musulmin suka zama kamar mikiya a cikin tsuntsaye, inda makiya addinin suka taso su a gaba.
Ustaz Babagana Malam Kyari ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya a garin Damaturu, inda ya ce rashin hadin kan Musulmi na kawo koma baya ga al’ummar, inda hakan ke ba da dama ga Yahudu da Nasara da sauran makiya addinin yin hawan kawara ga Musulmin duniya.
Malamin ya ce, ya zama wajibi al’ummar Musulmi su hada kansu in har suna son nasara ta ci gaba da tabbata a gare su “Domin a cikin Alkur’ani Mai girma Allah Ya ce mu yi riko da igiyar Allah kada mu rarraba, domin rarraba ba abin da za ta haifar mana sai asara duniya da Lahira. Don haka hadin kai shi ne babban tushen ci gaban al’umma,” inji shi.
Ustas Malam Kiyari ya ce, akwai bukatar hadin kan ya faro daga malamai domin kowane malami na da mabiyan da yake jagoranta, kuma matukar malaman suka hada kansu hadin kan mabiya ba zai yi wuya ba.
Ya ce su a garin Damaturu kusan dukan bangarorin malamai kansu a hade yake ta
yadda duk abin da ya taso ga daya daga cikin bangarorin mabiya kan hadu baki ya zo daya don yin magana da murya daya babu zancen wannan ko
wancan dan kungiya kaza ne.
Ya ce hanyoyin hadin kan al’ummar Musulmi na cikin nuna son juna da kaunar juna kamar yadda Allah Ya shimfida su, kuma manyan malamai da shehunan addini su yi kokari su hada kansu tare da dinke barakar da ke tsakaninsu ta yadda za su kawar da fifita sashi ko zargin juna domin daga na gaba a kan ga zurfin ruwa.
Kuma ya shawarci fallayen gwamnati uku wato tarayya da jihohi da kananan hukumomi
musamman Gwamnatin Tarayya cewa idan har za su kira taron hadin kai ko makamancin haka, bayan sun kira shugabanni kuma a nemo bangarorin shugabannin addini da manyan limamai sa su cikin zaman don isar da sakon ga ga al’umma.