Tilas Najeriya ta kasance a dunkule – Jonathan

A wani abu mai kama da martani ga masu gwagwarmayar neman kafa Jamhuriyyar Neja-Delta da sauran masu kiraye-kirayen a raba kasar nan, tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan y ace tilas ne Najeriya ta ci gaba da kasancewa a dunkule domin hakan ne mafi alheri.Dokta Goodluck Jonathan ya bayyana haka ne ga manema labarai a […]

Tilas Najeriya ta kasance a dunkule – Jonathan

A wani abu mai kama da martani ga masu gwagwarmayar neman kafa Jamhuriyyar Neja-Delta da sauran masu kiraye-kirayen a raba kasar nan, tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan y ace tilas ne Najeriya ta ci gaba da kasancewa a dunkule domin hakan ne mafi alheri.
Dokta Goodluck Jonathan ya bayyana haka ne ga manema labarai a shekaranjiya Laraba bayan ya yi ganawar sirri ta minti 20 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasar da ke Abuja.
Dokta Jonathan ya kuma tabbatar da cewa yana hada hannu da sarakunan gargajiya da sauransu wajen kwantar da kurar da ke tashi a yankin Neja-Delta.
Matsayin na Dokta Jonathan yana magana ne a daidai lokacin da ’yan ta’addan Neja-Delta na kungiyar Niger Delta Abengers (NDA) suke ta sanya bama-bama wa bututun mai da gas a yankinsu, sannan a daidai lokacin da wata kungiya mai suna Adaka Boro Abengers (ADA) ta ayyana ranar Litinin da ta gabata a matsayin ranar da za ta bayyana kafa Jamhuriyyar Neja-Delta. Sai dai bikin bai gudana ba sakamakon bayyanar dimbin sojoji a garin Kaiama da sauran wurare a yankin.
Da aka tambaye shi kana bin da yake yi wajen dakatar da daukar makamai a yankin, Dokta Jonathan ya ce: “Abin ba na ni kadai ba ne, ya hada da sarakunan gargajiya da dattawa da sauran masu fadi-a-ji da suka fito daga kabilar Ijaw. Muna tuntubar juna don ganin zaman lafiya ya dawo a kasar nan.”
Ya kara da cewa:  “Wadanda suke bibibiyar kalamaina daga cikinku lokacin da nake nan, abin da nake nanatawa shi ne muna bukatar dunkulalliyar Najeriya, kuma kullum ina nuna cewa Najeriya babbar kasar ce ba wai kawai saboda man fetur ba, domin akwai kasashe da dama da suke samar da man fetur amma ba a san da su ba. Mu babbar kasa ce saboda girmanmu da yawan jama’ar da muke da su, da yawan kabilun da muke da su, da za mu karkasa kasar zuwa kananan kasashe duniya za ta manta da mu.”
Dokta Jonathan ya kuma ce: “Wannan shi ne matsayina kuma idan babu zaman lafiya ba za a samu ci gaba ba a ko’ina a duniya. Muna aiki tare don ganin an warware matsalolin.”
Sai dai ya ki ya yi magana kan yaki da cin hanci da rashawa na wannan gwamnati da ke bankado munanan ayyukan da aka tafka a zamanin gwamnatinsa. “Ba zan yi magana a kan batun ba, saboda akwai shari’o’i da dama a gaban kotu, ba adalci ba ne in yi magana a kai. Amma zan yi magana a lokacin da ya dace lokacin da aka gama wadannan shari’u,” inji tsohon Shugaban kasar.
Ya bayyana cewa ya ziyarci Shugaba Buhari ne domin ya shaida masa irin ayyukan da ya gudanar a kasashen duniya musamman nada shi da aka yi baya-bayan nan na jagoran sanya ido na Tarayyar Afirka a kasar Zambiya.
Ya ce wannan al’ada ce da take gudana da tsofaffin shugabannin kasar nan, kuma ya ce ya sha zuwa ya gana da Shugaba Buhari wani lokaci ma cikin dare.