‘Tilas a biya masu gadi da ’yan aikin gida albashin N70,000 mafi ƙaranci’

Ko mai gadi aka ɗauka wajibi ne a biya shi albashin da bai gaza N70,000 ba.

‘Tilas a biya masu gadi da ’yan aikin gida albashin N70,000 mafi ƙaranci’

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa dukkanin ma’aikatan gwamnati da na masu zaman kansu sun cancanci Naira 70,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci.

Shugaban Majalisar ya ce cikin waɗanda suka cancanci sabon albashi mafi ƙaranci a ƙasar har da ’yan aikin gida, masu gadi, da direbobi da daidaikun mutane ke ɗauka a gidajensu.

Sanata Akpabio ya faɗi hakan ne yayin zaman yau Laraba bayan Majalisar Dattawan ta tabbatar da ƙudirin sabon albashi mafi ƙaranci a matsayin doka.

Shugaban Majalisar ya ce ko da mutum ya kasance tela ne amma ya ɗauki yara masu taya shi aiki a shago, tilas ne a biya su Naira 70,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.

Kazalika, Sanata Akpabio ya ce idan mace mai juna biyu ta haihu kuma ta buƙaci wadda za ta riƙa taya ta reno, tilas ne ita ma mai renon a biya ta albashi mafi ƙaranci da ya shafi ko wane ɓangare a ƙasar.

Da yake ci gaba da jawabi, Sanata Akpabio ko da hayar direba, ko mai gadi aka ɗauka, wajibi ne a biya su albashin da bai gaza N70,000 ba.

Ya bayyana farin cikinsa kan wannan sabuwar doka ta albashi mafi ƙaranci da aka zartar a ƙasar.

Ya kuma taya Ƙungiyar Ƙwadago da dukkanin ’yan Nijeriya da ma Majalisar Tarayya murna dangane da sabon albashi mafi ƙaranci.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe