Tilasta wa malaman makaranta yin rajista

Wani rahoto da Hukumar Yi Wa Malaman Makaranta Rajista ta Najeriya (NTRC) ta fitar kwanan nan ya nuna cewa malaman makaranta miliyan daya da rabi ne kadai suke da rajista da hukumar a kasar nan. Wannan kuwa babban abin takaici ne da tsoratarwa, musamman idan muka yi la’akari da yawan malaman da ake da su, […]

Tilasta wa malaman makaranta yin rajista
Tilasta wa malaman makaranta yin rajista

Wani rahoto da Hukumar Yi Wa Malaman Makaranta Rajista ta Najeriya (NTRC) ta fitar kwanan nan ya nuna cewa malaman makaranta miliyan daya da rabi ne kadai suke da rajista da hukumar a kasar nan. Wannan kuwa babban abin takaici ne da tsoratarwa, musamman idan muka yi la’akari da yawan malaman da ake da su, da kuma wadanda jami’o’i da kwalejojin ilimi ke ta yayewa duk shekara. Shugaban Hukumar, Farfesa Josiah Ajiboye ya bayyana cewa adadin malaman da suka yi rajista ya gaza kwarai daga yadda ya kamata a ce an yi wa rajistar.
Akwai bukatar malaman makaranta su yi rajista da hukumar domin a rika kula da tantance su. Abin da Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana ke nan ga ’yan jarida a lokacin da yake kaddamar da wani shiri na musamman na bunkasa ilimi a Najeriya a Abuja. Ya ce a bisa wannan tsari, malaman da suka kware kuma suka yi rajista da hukumar ne kadai za a amince wa aikin koyarwa a kasar nan.
Ministan ya bayyana cewa darajar aikin koyarwa ta fadi kasa warwas, don haka akwai bukatar a farfado da ita, wanda ta haka ne za a habaka da inganta harkokin ilimi a kasar nan. “Darajar tsarin samar da malaman makaranta sai faduwa take, musamman saboda wadanda ba kwararru ba sun samu kansu a matsayin malaman makaranta. Saboda haka, tantancewa da yi wa malaman makaranta na kwarai rajista zai taimaka wajen daidaitawa da dawo da martabar malaman makaranta da kuma inganta aikin koyarwa a kasar nan, kuma haka zai ba da damar a sallami duk wanda ba kwararre ba ne daga harkar koyarwa. Don haka, ba a yarda a dauki kowa a matsayin malamin makaranta ba, idan har bai da kwarewa da cancantar koyarwa. Babu wani saddabaru, idan ba ka cancanta ka koyar ba, ba za ka iya koyarwa ba,” inji Minista Adamu.
Tabbas akwai bukatar a tabbatar da cewa babu wanda zai zama malamin makaranta sai wanda ya samu kwarewa a aikin, domin kuwa babu wata kasa da za ta ci gaba kuma ta bunkasa ba tare da ilimin al’ummarta ba. A tsawon shekarun nan, ilimi ya tabarbare a kasar nan, inda ake samun dalibai na faduwa jarabawar karshe ta sakandare. Wannan ne kuma yake haddasa yadda ake samun yaye dalibai marasa hazaka daga jami’o’inmu duk shekara. Babu wata hanya da za a magance haka illa a koma can farko, a magance harkar koyo da koyarwa ta hanyar inganta malaman makaranta. Matukar gwamnati da gaske take yi na inganta ilimi a kasar nan, to lallai ne ta maida hankali wajen samar da ingantattu kuma kwararrun malamai masu yawa a kasar nan.
Idan aka ce an yi wa dukkan malaman makaranta rajista a hukumance, to wannan zai sanya a gano inda matsala take idan ta faru, musamman idan ana samun matsaloli a bangaren koyo da koyarwa, ta haka za a gano mai laifin faruwar haka a bangaren malaman. Wannan rajista kuma za ta ba hukuma damar gano malaman da ke bukatar komawa makaranta domin su koyo abin da ya dace da su koyar da dalibansu. Abin takaici, a yanzu aikin koyarwa ya zama na kowa, inda kowa ma zai iya shiga aji ya koyar saboda babu tantancewa daga hukumar da ta kamata.
Harkar koyarwa tana da matukar muhimmanci, ta yadda bai kamata a ce an bar ta kara-zube ba, yadda wanda bai samu aiki ne kadai zai ce zai yi ta ba. An dade ana samun karuwar bara-gurbin malaman makaranta a makarantun kasar nan. Haka kuma an sha samun batun yadda wadansu malaman ke taimaka wa dalibai wajen magudin jarabawa. Ta hanya daya ce za a iya gano malaman da ke almundahana, wannan kuwa ita ce hanyar taskancewa da tantance sunayen dukkan malaman makarantar da ke kasar nan a hukumance. Don haka, wannan hukuma, bai kamata aikinta ya tsaya wajen yi wa malamai rajista kadai ba, ya kamata aikinta ya hada da na tsara su da tura su guraben aiki a ko’ina cikin kasar nan da kuma tabbatar da cewa ana aiki da tsarin koyarwar da ya dace a ko’ina cikin kasar nan. Haka kuma, ya kamata hukumar ta sake bayyana ka’idojin da suka kamata malami ya mallaka, kafin a dauke shi aikin koyarwa, kamar yadda Hukumar Ilimi ta shar’anta. Wannan zai sanya sai wanda ya cika ka’ida ne za a yi wa rajista a matsayin malamin makaranta. Ke nan ya kamata hukumar ta fito da tsare-tsaren ci gaba da yi wa malaman rajista ta hanyar hadin gwiwa da kungiyar Malamai Ta kasa da kwalejoji da jami’o’in ilimi. Haka kuma a sanya ka’idar cewa sai mai rajista ne za a dauka aikin koyarwa. Gwamnati kuma ya kamata ta duba yiwuwar inganta albashi da alawus-alawus na malaman makaranta, yadda aikin zai zama mai tagomashi, ba kamar yanzu ba da babu romo a ciki!