Tinubu a Kano: Ko gaisuwa ce da neman iri?
Yadda aka yi Tinubu yake shiri da Ganduje amma suka bata da Buhari
A yayin da ake ganin Shugaba Buhari da Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun raba gari, dasawar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da kowannensu ta haifar da tambayoyi kan matsayin gwamnan a siyasance.
Ana ganin Ganduje shalelen Shugaba Buhari ne a cikin gwamnoni; sai Karuwar dasawarsa da Tinubu a baya-baya, inda ya yi uwa ya yi makarbiya wurin gudanar da taron cikar Tinubu shekara 69 a Kano, ta Kara jan hankali game da musabbabin hakan. Kusancin nasu ya sa wasu ke ganin Gwamnan Kano tamkar kadangaren bakin tulu – idan ana batun matsayin Buhari da Tinubu. To me ya sa kowannensu ke ji da shi duk da ana zargin cewa ba su shiri?
Sharar fagen zaben 2023
Aminu Muhammad Adam na da ra’ayin cewa: “Tinubu bai dace ya mulki Kasar nan ba domin bai yarda da Kasar a matsyain Kasa guda ba.
“Najeriya kasa ce da ake neman hadin kai. Idan zan iya tunawa akwai wata tattaunawa da Tinubu ya yi da jaridar Thisday a ranar 13 /4/1997, inda ya ce shi bai yarda da Najeriya a matsayin kasa daya ba.
“Ga duk mai hankali ya san furta irin wadanann kalamai cin amanar Kasa ne.”
Ibrahim Suraj a Kaduna ya ce, ba abin mamaki ba ne ganin Tinubu na shiri da Gwamnan Jihar Kano, duba da matsayin jihar a Arewa a zaben Shugaban Kasa.
“Ita ce jihar da ta fi yawan masu zabe a Najeriya; don haka yana bukatar Gwamnan Kano domin samun kuri’un jihar. Kowa ya san muhimmancin gwamnoni wurin cin zabe a jihohi.”
Kasuwar bukata ce
Dokta Khalifa Dikwa, malamin jami’a kuma mai sharhi kan al’amura, ya ce tun da farko, biri ya yi kama da mutum yadda Ganduje ya nuna wa bangaren Kudu maso Yamma cewa yana tare da su.
“Kafin ka je da nisa, auren ’yarsa da ya yi, ya riga ya nuna cewa ana tare ba shi da matsala da su, shi ya sa Tinubu ya natsu da shi fiye da sauran gwamnonin Arewa, duk cikinsu babu wanda ya yi yadda Ganduje ya yi.”
“Ni tun da na ji Ganduje a matsayinsa na dan Arewa, Bafulatani yana cewa a haramta yawon yin kiwo, na san ruwa ba ya tsami banza,” inji Joshua.
Yayin da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wanda ake hasashen zai yi wa Tinubun mataimaki idan har tarkonsu ya kama kurciya, ya ce siyasa babu ruwanta da addini ko Kabila.
“Idan da Allah Ya so sai ya yi mu cikin addini guda wanda kuma babu mai hana haka, kuma da Allah Ya so da ya yi mu duka Kabila guda wanda kuma hakan zai iya faruwa ba tare da wata matsala ba, domin kuwa babu wanda ya zabi addininsa ko kabilarsa.”
Wadanann kalamai da Gwamnan ya yi ya kara fito da zargin da ake yi cewa taro ne kawai na shimfida wa Tinubun katifar neman goyon baya, domin ya gaji Buhari.
A lokacin taron, Tinubu ya ce ya zabi Jihar Kano domin gudanar da bikin ranar haihuwarsa ne da zimmar hadin kan Kasa, wanda yake kallon a matsayin uwa daya uba daya.
Sai dai Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya yi takarar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, karKashin Jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya ce bai yarda cewa Tinubu ya shirya taron domin hada kan kasa ba.
Ya ce akwai abubuwa da dama da suka faru a kasar nan da ya kamata Tinubu ya fito ya nuna shi Shugaba ne na kwarai amma ya yi gum da bakinsa.
“A baya-bayan nan, an yi mummunan rikici a Shasa da Ibadan, da ke yankinsa na Yamma, inda aka kashe mutane da dama amma bai fito ya ce komai ba.
“A wurina, taron da Tinubu ya yi a Kano, ya nuna an yi taron ne domin siyasar 2023. APC da Tinubu sun gaza, don haka babu abin da za su ce wa ’yan Najeriya. A kullum rayukan al’umma na salwanta ba dalili, ba yankin Kudu maso Yamma kadai ba.
“Karara yunkurinsa ne na tsayawa takarar shugabancin Kasar nan a zaben 2023.’’
Da yake mayar da martani, mashawarcin Gwamna Ganduje kan harkokin mulkiDokta Abbati Bako ya ce masu sukar su kan batun ba su fahimci siyasar Najeriya ba.
“Gayyatar da aka yi wa Tinubu an yi ta ne da kyakkyawar niyya domin hadin kan Najariya.
“Kowa shaida ne duniya ma ta shaida cewa Mai Girma Gwamna Ganduje dan kishin kasa ne, mai son hadin kan kasa ne, mai kuma son ganin an zauna lafiya a kasar nan don haka don ya yi wannan ba wani abu ba ne.”
Duk hasashe ne – Khalifa Dikwa
Khalifa Dikwa ya ce, idan ma har Tinubu ya dauki Ganduje, to raunin gwamnan ne ya sa zai dauke shi, domin “mutum mai rauni suke zaba wanda za su iya juyawa saboda kar a yi irin na Obasanjo da Atiku.”
Game da tasirin Ganduje a 2023 a matasyin Gwamnan jihar da ke mafi yawan kuri’u, Khalifa Dikwa ya ce: “Ganduje yana da rauni kuma ba shi da farin jinin da ake bukata; idan har zai kai labari, to dole sai ya yi sulhu a gida da irinsu Kwankwaso da sauransu.”
Amma a ganin Muhammad Yahuza ‘sulhu’ “abu mai sauki ne a wurin ’yan siyasa, cikin dan lokaci za su yi shi.”
Sai dai Dokta Dikwa ya ce ba ya ganin Tinubu zai dauki Gwamnan Kanon mataimaki.
“A yanayin da kasar nan take ciki, abu ne mai wuya a iya tsayar da dan takarar Shugaban Kasa da Mataimakinsa Musulmi zalla ko Kirista zalla,” a cewarsa.
“Wata sarKaKiyar” a cewarsa, ita ce, “Kananan kabilu a kasar da kuma Arewa ta Tsakiya suna son Mataimakin Shugaban Kasa ya fito daga cikinsu tun da Arewa ta Yamma da Arewa ta Gabas sun yi.”
Buhari ba ya fada da Tinubu
Sai dai ya ce babu zaman doya da manja tsakanin Buhari da Tinubu, “‘Cabal’ (’yan fada) ne da ke ganin ba za a yi da su ba suke namen kange shi Tinubun daga kaiwa labari a 2023.
“Idan kuma ba su samu yadda suke so ba, to za su iya ballewa daga APC su ma kafa wata sabuwar jam’iyyar.”
Game da yiwuwar Buhari ya goya wa Sanata Tinubu baya a 2023, ya ce, “A zahirin gaskiya babu wanda Buhari zai goya wa baya, shi mutum ne da yake ganin a bar komai yadda yake ba sai an zabi wani ba.”
Kware wa Buhari baya
Wasu na ganin Tinubu ya riga ya bayyana maitarsa ta neman kujerar Shugaban Kasa, amma ba zai yiwu ya kware wa Shugaba Buhari baya ba domin samun karbuwa.
Duk gazawar gwamnatin, shi ne ya tallata wa ’yan Najeriya ita tun da farko kuma jam’iyyarsu daya, saboda haka idan ya kushe ta, to ya daba wa kansa wuKa.
Amma yana buKatar ya fito ta wata siga da za a gamsu cewa ya damu da halin da kasar take ciki na matsalar tsaro da rashin ayyukan yi da matsin rayuwa da dangoginsu.
Abin jira a gani shi ne nan da lokacin da za a kada kugen zaben 2023, a ga kowanne daga cikinsu ina ya karkata da kuma yadda za ta kaya.