Tinubu ba zai ci amanar Arewa ba —Badaru

Badaru ya ce Tinubu yana da koshin lafiya tun sa ya iya gudanar da aikin Umrah a kasa mai tsarki.

Tinubu ba zai ci amanar Arewa ba —Badaru

Gwamnan Jigawa, Mohammad Badaru Abubakar

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya karyata rade-radin da ke cewar idan dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ci zabe, zai fi mayar da hankali wajen inganta Kudancin Najeriya.

Gwamnan ya ce tarihin dan takarar ya nuna ba zai aikata abin da ake alakanta shi da shi ba.

“Maganar da ake game da lafiyarsa, ziyarar da muka je Makkah don yin Umrah, ya yi Dawafi ya kuma yi Sa’i, hakan ya nuna irin cikakiyar lafiyar da yake da ita.

“Ya kamata ’yan Najeriya su gane cewa an wuce zamanin ci da addini, bangaranci ko kabilanci a siyasa.

“Duk abubuwan da ake fada a kan Bola Tinubu ba komai ba ne face karyayyaki daga wadanda ba za su iya cin zabe ba face sai sun yi kokarin dakile daukakar dan takarar APC,” in ji Badaru.

Ya bayyana hakan ne a Kano, yayin da dan takarar na APC ya gana da malaman addinin Musulunci daga Arewa Maso Yamma a ranar Talata.

Kazalika, Badaru ya ce duk abubuwan da Tinubu ya yi game da shirye-shiryen takararsa, ya yi ne da hadin guiwar gwamnan na Jigawa, Ganduje da kuma Nuhu Ribadu wadanda dukkaninsu sanannu ne a fagen siyasar Najeriya.

’Yan adawa musamman jam’iyyar PDP, na sukar takarar tsohon gwamnan na Jihar Legas da cewa ba shi da cikakiyar lafiyar da zai iya jagorantar Najeriya idan ya lashe zaben 2023.