Tinubu ba zai sauya tsare-tsaren gwamnatinsa ba —APC

APC ta buƙaci PDP ta haɗa hannu da Gwamnatin Tinubu domin inganta rayuwar al’ummar Najeriya.

Tinubu ba zai sauya tsare-tsaren gwamnatinsa ba —APC

Jam’iyyar APC mai mulki ta ce Gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta da aniyar sauya tsare-tsarenta da manufofinta na kawo cigaban ƙasa.

APC ta kuma buƙaci babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da tunanin Tinubu zai sauya tsare-tsaren gwamnatinsa, tana mai kira ga jam’iyyar adawar ta hada hannu da gwamnati domin inganta rayuwar al’ummar Najeriya.

Ta kuma ƙaryata zargin da PDP ke mata na murɗe zaɓen gwamnan Jihar Edo da zummar mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya guda.

Idan ba a nanata ba Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya zargi APC da murɗe zaɓen na Edo a ƙoƙarinta na ganin mulki a Najeriya ya koma hannun jam’iyya ɗaya kacokan.

Abba ya yi tafiya yayin da rikici ya dabaibaye NNPP a Kano

Kotu ta hana EFCC kama tsohon minista kan taƙaddamar fili

Isra’ila ta ɗaiɗaita yara sama da 400,000 a Lebanon — UNICEF

Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso