Tinubu bai cire tallafin mai ba —Keyamo

Keyamo ya ce kasafin kudin 2023 da Tinubu ya gada daga Gwamnatin Buhari bai yi tanadin biyan kudin tallafin man fetur ba.

Tinubu bai cire tallafin mai ba —Keyamo

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo

Minista a Ma’aikatar Kwadago da Kyautatuwar Ayyuka, Festus Keyamo ya ce Shugaba Bola Tinubu bai cire tallafin man fetur ba.

Keyamo ya bayyana cewa, kasafin kudin da Tinubu ya gada daga Gwamnatin Buhari ne bai yi tanadin biyan tallafin man ba.

A yayin jawabinsa na farko a dandalin Eagles Square, Tinubu ya ce tallafin man fetur ya tafi ke nan.

Bayan sanarwar tasa, wasu gidajen mai sun kara farashi, lamarin da ya haddass dogayen layuka a gidajen mai a fadin Najeriya.

Amma da yake mayar da martani, Keyamo ya ce ba a fahimci jawabin na Tinubu ba ne.

Keyamo ya wallafa a Twitter cewa: “Wasu ’yan jarida ba su fahimci jawabin Tinubu ba. Kuskure ne su ce Gwamnatin Tibubu ce ta Cire tallafin mai. Gwamnatin dai ta gaji kasafin 2023 wanda babu tanadin tallafi mai a ciki.

“Shugaba Tinubu ya amince da wannan yanayin ne kawai a jawabinsa na farko a dandalin Eagle Square.

“Don haka duk wani mai neman tallafin ya kamata ya gamsar da ’yan Najeriya dalilin da ya sa Shugaba Tinubu zai fara da rashin bin doka ta hanyar yin alkawarin dawo da wani abu da doka ta cire.

“Wadanda ke da’awar kare hakki ko jin dadin ma’aikata, ya kamata su gamsar da ’yan Najeriya cewa Dala biliyan 10 da ake kashewa ba ya kawo koma baya ga tattalin arzikin kasa.

“Wannan ita ce tattaunawar da ’yan Najeriya ya kamata su shirya yi yanzu.”

Kwamishina ya yi murabus bayan sauya masa ma’aikata a Kano

Gobara ta ƙone shaguna 50 a kasuwar kara a Sakkwato

An yi canjaras tsakanin Liverpool da Manchester United

Tinubu zai tafi Ghana rantsar da John Mahama