Tinubu bai damu da halin da al’umma ke ciki ba — PDP

Masharhanta da dama sun soki jawabin Tinubu, inda suka ce ya gaza taɓo buƙatun masu zanga-zangar kai-tsaye.

Tinubu bai damu da halin da al’umma ke ciki ba — PDP

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce jawabin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar Lahadi, kan zanga-zangar ƙuncin rayuwa da yunwa a ƙasar nan bai taɓo abubuwan da masu zanga-zangar suke kokawa a kai ba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, wadda Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Kasa, Mista Debo Ologunagba, ya sa wa hannu, Jam’iyyar PDP ta ce “Jawabin na Shugaba Tinubu ya nuna yadda ƙarara, Jama’iyyar APC da Shugaba Tinubu ba su damu da halin ƙunci da al’ummar ƙasar nan ke fama da shi ba.

Shugaba Tinubu dai ya yi jawabin ne kwana huɗu bayan da matasa suka fantsama kan tituna don nuna fushi kan halin matsi da al’umma ke fama da shi.

A cikin jawabin, Shugaba Tinubu ya buƙaci al’umma su yi haƙuri su dakatar da zanga-zangar ganin cewa ta yi sanadiyyar rasa rayuka a wasu jihohi.

Zanga-zangar wadda ta fara a ranar Alhamis ta rikiɗe zuwa tarzoma a wasu jihohi, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyar al’umma.

Sanarwar da Jam’iyyar PDP ta fitar ta ci gaba da cewa “Jam’iyyar ta ji takaicin yadda Shugaban ya kasa bayyana matakan da ya kamata a ce gwamnati ta ɗauka domin kawo wa al’umma sauƙin matsin da suke ciki.

“Shugaban Kasar ya kasa yin bayani kan buƙatun al’umma na ɗaukar matakan da za su rage tsadar man fetur da magance faɗuwar darajar Naira da kuma samar da abinci ga al’ummar da ke cikin yunwa,” in ji sanarwar.

Shugaba Tinubu a jawabin nasa, ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakai kamar na shirin bai wa ɗalibai bashin karatu da raba wa jihohi maƙudan kuɗaɗe da kuma bayar da tallafin abinci ta hannun gwamnoni.

Sai dai masharhanta da dama sun soki jawabin na Shugaba Tinubu, inda suka ce ya gaza taɓo buƙatun masu zanga-zangar kai-tsaye.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka zargi jami’an tsaro da bude wuta a kan masu zanga-zangar kuma sun buƙaci hukumomi su yi bincike a kai.

HOTUNA: Tankar mai ta yi bindiga a Dikko Junction

An kashe manyan alƙalai 2 a harabar Kotun Ƙolin Iran

’Yan Yahoo sun harbe jami’in EFCC har lahira a bakin aikinsa

Farashin kayan abinci ya faɗi warwas a Neja