Tinubu da Atiku sun yaba da hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin ƙananan hukumomi

Tabbatar da ’yancin ƙananan hukumomi babbar nasara ce ga ’yan Najeriya.

Tinubu da Atiku sun yaba da hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin ƙananan hukumomi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba da hukuncin Kotun Ƙoli da ta tabbatar da ’yancin ƙananan hukumomi.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar bayan hukuncin a ranar Alhamis, shugaban ya ce hukuncin tamkar jaddada matsayin ƙaramar hukuma ne a Kundin Tsarin Mulki.

A hukuncinta na ranar Alhamis, Kotun Ƙolin ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki.

Alƙalin da ya jagoranci hukuncin Emmanuel Agim ya ce ƙananan hukumomi 774 na Najeriya su ke da haƙƙin tafiyar da kuɗaɗensu da suke samu daga kason Tarayya.

Shugaba Tinubu ya ce wannan mataki ne da ya tabbatar da matsayin ƙaramar hukuma a matsayin ɓangare na gwamnati da kuma tabbatar da shugabanci nagari.

Ya ce rashin sakin mara ga ƙananan hukumomi babbar matsala ce ga ci gaban ƙasa musamman yadda ba a jin tasirin gwamnati a karkara.

Shi ma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya ce hukuncin da Kotun Ƙoli ta zartar kan tabbatar da ’yancin ƙananan hukumomi babbar nasara ce ga ’yan Najeriya.

Atiku ya yaba da hukuncin ne a bayanin da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.

Atiku ya ce hukuncin Kotun Ƙoli mataki ne a tafarkin da ya dace kuma babban gyara ne ga tabbatar da ci gaba a sassan ƙasar.

Wazirin Adamawan ya ce matakin haɗa kason kuɗaɗen jiha da na ƙananan hukumomi ya samo asali ne daga son rai na siyasa.

“Na goyi bayan matakin Kotun Ƙoli cewa tsarin gwamnati ya kafu ne a mataki uku, kuma ƙananan hukumomi ne ya kamata su kasance cibiyar tabbatar da ci gaba,” a cewar Atiku.

Ya ƙara da cewa hatta kuɗaɗen shiga da ƙananan hukumomin ke samarwa su kasance sun tafi kai-tsaye zuwa asusunsu.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara