Tinubu da gwamnoni 6 sun tafi Jamhuriyyar Benin

Shugaba Patrice Talon da kansa ya gayyaci gwamnoni 6 da ke cikin tawagar Tinubu.

Tinubu da gwamnoni 6 sun tafi Jamhuriyyar Benin

Shugaba Bola Tinubu ya sauka a birnin Cotonou don halartar bikin cika shekara 63 da samun ’yancin Jamhuriyar Benin.

Benin ta samu ’yancin kai ne daga Faransa a ranar 1 ga watan Agustan 1960, wata biyu kafin Najeriya ta samu nata ’yancin.

Sanarwar da Fadar Shugaban Kasar ta fitar na cewa cikin tawagar shugaba Tinubu akwai gwamnoni guda shida, wadanda Shugaba Patrice Talon ya gayyata da kansa.

Gwamnonin sun hada da Dapo Abiodun na Jihar Ogun da Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas da Seyi Makinde na Oyo da AbdulRahman Abdulrazaq na Kwara da Nasir Idris na Kebbi da kuma Mohammed Bago na Jihar Neja.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota